Tallafin N50,000: SERAP Ta Jero Tambayoyin da ke Bukatar Amsa daga Gwamnatin Tinubu

Tallafin N50,000: SERAP Ta Jero Tambayoyin da ke Bukatar Amsa daga Gwamnatin Tinubu

  • SERAP ta aika wa Ministan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Bernard Doro, buƙatar bayyana kuɗaɗen shirin NERSI da yadda ake gudanar da shi
  • Ƙungiyar ta nemi gwamnati ta fayyace ko tallafin N50,000 na biyan sau ɗaya ne ko kuma za a rika bayar da shi duk wata
  • SERAP ta gargaɗi gwamnati kan yiwuwar amfani da tallafin wajen neman goyon bayan siyasa gabanin zaɓen shekarar 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ƙungiyar kare haƙƙin jama'a da tabbatar da riƙon amana a harkokin tattalin arziki da zamantakewa, SERAP, ta buƙaci gwamnatin tarayya ta bayyana cikakken bayani kan yadda take gudanar da shirin tallafin N50,000 na National Emergency Relief and Stabilisation Intervention (NERSI).

Ƙungiyar ta buƙaci Ministan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Dakta Bernard Doro, ya bayyana yadda ake zaɓen waɗanda za su amfana, tsarin biyan kuɗin da kuma yarjejeniyoyin da aka ƙulla da kamfanonin hada-hadar kuɗi ta intanet.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta fadi abubuwa 3 da masu son samun tallafin N50,000 za su kiyaye

SERAP ta tambayi Tinubu kan tallafin
Mai girma Bola Ahmed Tinubu, shugaban kasar Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

SERAP ta gabatar da wannan buƙata ne ta hanyar wasiƙar neman bayanai ƙarƙashin dokar 'yancin samun bayanai mai ɗauke da ranar 7 ga Nuwamba, 2026, cewar rahoton jaridar The Punch.

Mataimakin daraktan ƙungiyar, Kolawole Oluwadare, ne ya sanya wa wasiƙar hannu.

SERAP ta nemi cikakken bayani kan kuɗaɗen shirin

Buƙatar ta biyo bayan sanarwar da ma'aikatar ta fitar ranar 30 ga Oktoba, inda ta bayyana shirin NERSI da nufin tallafa wa 'yan Najeriya masu fama da matsin tattalin arziki da N50,000.

Sai dai SERAP ta ce akwai muhimman tambayoyi da har yanzu ba a amsa ba, musamman game da jimillar kuɗin da aka ware wa shirin, jihohin da zai shafa da kuma tsawon lokacin gudanar da shi.

Ƙungiyar ta kuma nemi ministan ya bayyana yadda ake zaɓen waɗanda za su amfana daga rajistar gidajen da ke cikin mawuyacin hali ta ƙasa (National Social Register) da bayanan shaidar ɗan ƙasa da aka tantance.

Kara karanta wannan

Dama ta samu: Opay ya bayyana yadda masu kananan wayoyi za su nemi nemi tallafin N50,000

Ta buƙaci a bayyana adadin kuɗin da aka ware a kasafin kuɗi, waɗanda aka saki, da kuma waɗanda aka kashe wajen gudanar da shirin.

Haka kuma, ta nemi cikakken bayani kan ƙa'idojin cancanta, yadda ake tantance waɗanda za su amfana da kuma yadda aka rarraba su a sassa daban-daban na ƙasar.

Shin tallafin N50,000 na wata-wata ne?

SERAP ta kuma buƙaci ma'aikatar ta fayyace ko tallafin N50,000 biyan sau ɗaya ne ko kuma za a rika bayar da shi duk wata.

Ƙungiyar ta ce sanarwar da ma'aikatar ta fitar a baya ta bayyana cewa za a rika biyan tallafin duk wata, amma wani takardar amsa tambayoyi da aka fitar daga baya bai fayyace yawan lokutan biyan kuɗin ko tsawon lokacin shirin ba.

A cikin wasiƙar, SERAP ta ce:

“'Yan Najeriya na da 'yancin sanin yadda ake kashe kuɗaɗen gwamnati da aka ware wa shirin NERSI, waɗanda ke karɓar tallafin, yadda ake zaɓensu da kuma ko shirin yana isa ga mutanen da suka fi buƙatar taimako.”

SERAP ta gargaɗi gwamnati

Ƙungiyar ta kuma nuna damuwa kan yiwuwar wasu 'yan siyasa su yi katsalandan a shirin, musamman yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Tallafin N50,000: Gwamnatin Tarayya ta fitar da ka'idoji 4, ta ja kunnen 'yan Najeriya

Ta jaddada cewa dole ne a raba tallafin gwamnati bisa ainihin buƙatar mutane da ƙa'idojin cancanta masu ma'ana, ba tare da la'akari da jam'iyyarsu ko goyon bayansu ga wani ɗan siyasa ba.

SERAP na neman amsoshi kan tallafin N50,000
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Yankunan da za su amfana da tallafin N50,000

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi ƙarin haske kan ci gaba da raba tallafin N50,000 da aka yi ga yan Najeriya saboda rage masu radadi.

Gwamnatin ta bayyana cewa shirin tallafin Naira 50,000 na NERSI ya shafi gidaje masu ƙaramin ƙarfi a dukkan shiyyoyi shida na Najeriya, ciki har da jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng