Sarakunan Yarbawa Sun Yi Matsaya kan ‘Dan Takaran Shugaban Kasa da Tallafin Fetur
- Sarakunan gargajiya daga yankin Kudu maso Yammacin ƙasar nan sun yi watsi da kiran a dawo da tallafin man fetur
- A wani taro, sun bayyana goyon bayansu ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da manufofin tattalin arziƙinta
- Masu sarautar sun kuma buƙaci a ci gaba da tsarin karɓa-karɓar shugabancin ƙasa tsakanin Arewa da Kudu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Oyo - Sarakunan gargajiya daga yankin Kudu maso Yammacin Najeriya sun yi gargaɗi kan batun sake dawo da tsarin tallafin man fetur a Najeriya.
Sarakunan bayyana cewa maido tsarin tallafin ba zai amfani tattalin arziƙin ƙasar da kuma dorewar shigar kuɗin gwamnati na tsawon dogon lokaci ba.

Source: UGC
Sarakunan Yarbawa sun halarci taro a Oyo
Ma’aikatar labarai ta ce wannan na daga cikin matsayar da sarakunan suka cimma a wani taro da suka gudanar a fadar Olubadan na Ibadan, a jihar Oyo.
Sarakunan da suka halarci taron sun haɗa da Ooni na Ife, Adeyeye Ogunwusi; Olubadan na Ibadanland, Rashidi Ladoja da Aseyin na Iseyin.
Akwai Soun na Ogbomoso, Oba Afolabi Ghandi Olaoye; Olu na Ilaro, Oba Kehinde Olugbenla; Deji na Akure wato Oba Aladetoyinbo Aladewusi.
Sauran sun haɗa da Ebumawe na Ago Iwoye, Oba Abdilrasq Adenugba; Ewi na Ado Ekiti, Oba Rufus Aladesanmi; da kuma Owa Obokun Adimula
Bayanan da aka samu daga shafin ma’aikatar ya nuna Mai martaba Adesuyi Hastrup ya samu halarta.
Matsayar Sarakunan Yarbawa kan tallafin fetur
A cikin sanarwar haɗin gwiwa da aka fitar bayan taron, wadda Alake na Egbaland, Oba Gbadebo, ya karanta, sun nuna ba su tare da tallafin man fetur.
A madadin sauran sarakunan, majalisar ta ce ta fahimci halin tattalin arziƙin da ƙasar ke ciki, kuma tana goyon bayan matakin gwamnati na soke tsarin.
Sanarwar ta ce:
"Taron ya cimma matsayar cewa sake dawo da tallafin man fetur ba zai amfani ci gaban tattalin arzikin ƙasa da kuma dorewar kuɗin gwamnati a dogon lokaci ba."

Kara karanta wannan
Mataimakin shugaban majalisa ya ga ta kansa da ya yi ƙokarin tallata Tinubu a taron jama'a
Goyon bayan Bola Tinubu ya zarce a ofis
Gabanin zaɓen 2027, Daily Trust ta ce sarakunan Kudu maso Yamma sun kuma bayyana goyon bayansu ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Sarki Gbadebo Aremu da Ghandi Olaoye sun yaba da ƙoƙarin Gwamnatin tarayya wajen magance matsaloli da kuma aiwatar da shirye-shiryen raya ƙasa.
A cikin sanarwar, sarakunan sun ce:
"Majalisar ta sake tabbatar da cikakken goyon bayanta ga Mai Girma Shugaban Ƙasar Tarayyar Najeriya da gwamnatinsa."
Sun kuma bukaci sarakunan gargajiya da ke yankin su ci gaba da wayar da kan al'ummominsu domin su goyi bayan manufofi da shirye-shiryen gwamnatin APC.
Matsayar su kan mulki da 'yan sandan jihohi
Sarakunan sun kuma yi kira da a ci gaba da tsarin karɓa-karɓar shugabancin ƙasa tsakanin Arewa da Kudu, inda suka ce ya kamata shugabanci ya tsaya a Kudu.
Sun ce tsarin karɓa-karɓar mulki ya taimaka wajen tabbatar da daidaito, haɗin kan ƙasa da zaman lafiya.
Iyayen ƙasar sun kuma nuna goyon bayansu ga shirin kafa rundunar 'yan sandan jihohi, sun bayyana cewa hakan zai taimaka wajen ƙarfafa tsaron cikin gida.
Sun bukaci duk sarakunan gargajiya da su wayar da kan matasa su kasance cikin shirin cin gajiyar guraben ayyukan yi da sauran damarmakin da za a samu.

Source: Twitter
Bola Tinubu ya kore yiwuwar dawowar tallafin fetur
An ji labari cewa Shugaba Bola Tinubu ya nanata cewa ba za a dawo da tallafin fetur ba, lamarin da ya haifar da muhawara mai zafi a fagen siyasa.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya dage cewa idan ya samu mulkin Najeriya a 2027 a jam’iyyar ADC sai ya dawo da tallafin fetur.
A halin yanzu, ana sayar da litar fetur a Najeriya kan kusan N1, 500. Kafin gwamnatin Tinubu, ana sayar da litar fetur a tsakanin N185 ne zuwa N200.
Asali: Legit.ng

