Yusuf Datti da sauran ‘yan a mutun Peter Obi 10 da suka watsar da tafiyar shi

Yusuf Datti da sauran ‘yan a mutun Peter Obi 10 da suka watsar da tafiyar shi

Nigeria - Zuwa yanzu da shekarar 2026 ta ke shirin zuwa karshe, an samu shahararrun mutane da ‘yan siyasan da suka bar Peter Obi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Wasu da aka sani tare da Mista Peter Obi a jam’iyyar LP lokacin zaben 2023 ko kuwa tun a 2019 da yake jam’iyyar PDP sun raba jiha da shi.

Rabuwa da wadannan mutane ta raunana tafiyar Obidient da ta shahara musamma a Kudu maso yamma da kudu maso kudancin kasar.

Yusuf Datti Baba-Ahmed
Peter Obi da abokin takararsa a 2023 lokacin kamfen LP Hoto: Yusuf Datti Baba-Ahmed
Source: Getty Images

Jagororin Obidient da suka rabu da Peter Obi

Legit Hausa ta kawo manyan mutanen da Obidient ta rasa bayan zaben da aka yi a 2023.

1. Serah Ibrahim

Serah Ibrahim ta na cikin wadanda Obidient ta rasa kuma babu ita za a yi wa kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa a shekarar 2027.

Kara karanta wannan

An yi arangama da 'yan sba suka lai hari wurin taron magoya bayan Obi da Kwankwaso

Fitacciyar masaniyar tattalin kuma mai kare hakkin bil adama ta koma wajen Seyi Makinde, kuma da ita aka tsara manufofin jam’iyyar APM.

2. Doyin Okupe

Obi ya rasa mutumin da ya zama masa Darekta janar na yakin neman zaben shugaban kasar 2019 lokacin da ya tsaya takara a karkashin LP.

Dr. Doyin Okupe ya yi murabus daga jam’iyyar yana cewa akidunsa ba su dace da na jam’iyyar LP ba, bayan shekara guda da yin haka ya mutu.

3. Keneth Okonkwo

Shi Keneth Okonkwo sai da ya zama kakakin kwamitin yakin zaben Obi, amma wannan bai hana shi hakura da tafiyar Obidient tun a farkon 2024.

Tsohon ‘dan wasan kwaikwayon ya fito shafinsa na X yana nuna bai gamsu da salon tsohon mai gidansa ba, ya zarge shi da rauni wajen rikon LP.

4. Valentine Ozigbo

‘Dan kasuwa kuma ‘da siyasa Valentine Ozigbo bai cigaba da zama a jam’iyyar LP ba lokacin da rigingimu suka rutsa su da gabas da yamma.

Tsohon ‘dan takaran gwamnan na Anambra ya bi Obi daga PDP zuwa LP, amma bayan nan sai aka ji sanarwa cewa ya koma jam’iyyar APC mai-ci.

Kara karanta wannan

Amnesty ta bukaci a kama 'yan daban da suka kai wa Pantami hari a Gombe

5. Isaac Balami

Shi ma Isaac Balami ba a bar shi a baya cikin mutanen da suka tattara suka kyale ‘dan takaran shugaban kasar na NDC da tafiya ta yi tafiya a siyasa.

Daga baya Tribune ta rahoto cewa ya jagoranci matasan yankin Arewa maso tsakiya zuwa wajen Seyi Tinubu bayan zamansa darekta a kungiyar City Boy.

6. Adesina Fagbenro-Byron

A watan Oktoban nan sanarwa ta fito cewa Adesina Fagbenro-Byron ya tsallaka zuwa wajen Bola Tinubu, ya daina goyon bayan Obi a harkar siyasa.

Fagbenro-Byron lauya ne, yana cikin wadanda suka kafa jam’iyyar Kowa, yanzu kuma tsohon ‘dan Obidient din ya dage da tallar APC in ji The Nation.

7. Fabian Chukwudoruo

Fabian Chukwudoruo shi yake jagorantar wata kungiyar ‘Batified Obidients’ ta tsofaffin masoyan Peter Obi da suka yi ridda zuwa tafiyar Bola Tinubu.

The Cable ta rahoto tsohon darektan harkokin na Obidient kuma jagora a kamfen din Obi/Datti yana cewa Obi ba zai iya rike kasa irin Najeriya ba.

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban majalisa ya ga ta kansa da ya yi ƙokarin tallata Tinubu a taron jama'a

8. Nana Kazaure

Da Atiku Abubakar ya tashi fitar da ‘yan kwamitin yakin neman zama shugaban kasarsa a jam’iyyar ADC, sai aka ga har da sunan su Nana Kazaure.

Kafin nan tana cikin ‘yan gani-kashe-nin Mista Peter Obi kuma tana magana da yawun magoya bayansa, yanzu da su ake yi wa ADC kamfen 2027.

9. Yunusa Tanko

Duk kasancewarsa Mai ba Peter Obi shawara a kan harkokin siyasar Arewacin Najeriya, kwatsam aka ji jagoran kungiyar Obidient na kasa ya bar su.

Tanko Yunusa ya kasance cikin wadanda suka fi kowa kusanci da ‘dan siyasar, yanzu ya samu wuri a kwamitin yakin zaben Adewole Adebayo a SDP.

10. Yusuf Datti Baba-Ahmed

Na karshe yau a jerin namu shi ne babbansu, Yusuf Datti Baba-Ahmed wanda tuta guda ya rike tare da Mista Peter Obi a zaben shugaban kasar 2023.

Dr. Datti Baba Ahmed ya sanar da duniya ficewarsa daga LP zuwa PRP kuma an rika jin shi yana sukar salon shugabancin tsohon abokin takaransa.

Kara karanta wannan

'Maganar yunwa fa ruruta ta ake yi': Jigon APC ya magantu kan halin kunci

Yusuf Datti Baba-Ahmed
Peter Obi da Yusuf Datti Baba-Ahmed a hanyar yakin zaben 2023 a Najeriya Hoto: @PeterObi
Source: Facebook

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng