ADC ko APC: Kwankwasiyya Ta Fadi Jam'iyyun da Kwankwaso Ke Tattaunawa da Su
- Kungiyar Kwankwasiyya ta yi tsokaci kan tafiyar siyasar tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
- Kwankwasiyya ta bayar da tabbacin cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana tattauanwa da wasu jam'iyyun siyasa a Najeriya
- Mai magana da yawun Kwankwasiyya ya bayyana cewa ana yin tattaunawar ne domin samo jam'iyyar da za a yi amfani da ita gabanin babban zaben shekarar 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Ƙungiyar Kwankwasiyya ta tabbatar da cewa jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, yana tattaunawa da wasu jam'iyyun siyasa.
Kwankwasiyyya ta tabbatar da cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana tattaunawa da jam’iyyun ADC da NDC.

Source: Facebook
Kwankwaso na tattaunawa da jam'iyyun ADC, NDC
Mai magana da yawun ƙungiyar Kwankwasiyya, Mansur Kurugu, ya tabbatar da hakan ga jaridar Daily Trust a ranar Litinin, 23 ga watan Maris 2026.
Mansur Kurugu ya bayyana cewa tattaunawar na iya kaiwa ga haɗewar waɗannan jam'iyyu na siyasa.
A cewarsa, Kwankwaso da sauran shugabannin jam’iyyun ba su riga sun yanke shawara kan wace jam'iyya za su yi amfani da ita ba, yana mai jaddada cewa har yanzu ana tsaka da tattaunawa.
Mutanen da Kwankwaso ke tattaunawa da su
“Gaskiya ne cewa Kwankwaso yana tattaunawa da jam’iyyun ADC da NDC, kuma muna da kyakkyawan fatan cewa a karshe shugabannin za su dauki ɗaya daga cikin jam’iyyun kafin zaɓubbukan 2027.”
“Mutane irin su Seriake Dickson, Peter Obi, da Seyi Makinde duk suna cikin wannan tattaunawa, kuma an samu ci gaba sosai."
- Mansur Kurugu
Ya ƙara da bayanin cewa a ƙarshen tattaunawar, shugabannin za su ɗauki ko dai ADC, NDC, ko kuma ma NNPP a matsayin jam'iyyar da za su yi amfani da ita.
Kwankaso ya gana da manyan jiga-jigai
A ranar Lahadi ne Kwankwaso ya karɓi bakuncin gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde; tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi; da kuma jagoran jam’iyyar NDC na ƙasa kuma Sanatan Bayelsa, Seriake Dickson, a wani taron Sallah a Kano.

Source: Facebook
Duk da cewa ba su bayar da cikakkun bayanai kan ainihin dalilin ziyarar ba, masu sharhi da dama na ganin cewa hakan ba zai rasa nasaba da shirye-shiryen zaɓen shekarar 2027 ba.
Kwankwaso ya tura sako ga Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana matukar bakin cikinsa kan hare-haren kunar bakin wake da suka girgiza birnin Maiduguri.
Kwankwaso ya jaddada cewa lokaci ya yi da gwamnati za ta dauki mataki mai karfi maimakon nuna sakaci ko jinkiri wajen magance matsalar tsaro.
Ya bukaci gwamnatocin tarayya da na jihohi da su hada kai wajen samar da dukkanin kayan aiki da goyon bayan da ake bukata domin bai wa jami’an tsaro damar murkushe kungiyoyin ta’addanci gaba daya.
Asali: Legit.ng

