Zai Shiga APC ne? Sule Lamido Ya Bude Kofar Ganawa da Shugaba Bola Tinubu
- Sule Lamido ya bayyana cewa a shirye yake ya zauna da shugaban kasa, Bola Tinubu domin tattauna abin da zai kawo ci gaban Najeriya
- Tsohon gwamnan jihar Jigawa ya kuma musanta rade-radin da ake yadawa cewa an masa tayin shiga APC amma ya yi fatali da shi
- Wannan kalamai na zuwa ne yayin da rikicin PDP ke kara tsanani tsakanin bangaren ministan Abuja, Nyesom Wike da tsagin Tanimu Turaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bamaina, Jigawa – Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana cewa a shirye yake ya gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu idan aka gayyace shi, matukar hakan zai amfani hadin kai da ci gaban Najeriya.
Sule Lamido, wanda yana daya daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyar PDP a 1998, ya jaddada burinsa na warwrae duk wata matsala da ta addabi kasar nan don samun ci gaba.

Source: Facebook
Sule Lamido ya shirya haduwa da Tinubu
Lamido ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da jaridar The Nation a garinsu Bamaina a ranar Sallah, inda ya ce ba shi da wata matsala wajen tattaunawa da shugaban kasa idan hakan zai taimaka wa kasa.
“A shirye nake fiye da kowa, amma yaushe za mu tafi mu gan shi?” yana mai jaddada aniyarsa ta shiga tattaunawa mai amfani.
Lamido ya musanta zargin shiga APC
Sai dai tsohon gwamnan ya musanta rade-radin da ke cewa ya ƙi karbar gayyatar shiga jam’iyyar APC mai mulki, yana mai cewa ba a taba yi masa irin wannan tayin ba.
A ruwayar Daily Post, Lamido ya ce:
“Yaushe aka gayyace ni? Don Allah ku fada min. Shin ya aiko ku ne? Ni yanzu ne na fara jin wannan maganar.”
Lamido ya jaddada cewa duk wata hulda tsakaninsa da shugaban kasa ya kamata ta kasance ne bisa muradun kasa, ba wai siyasa ba.
“Idan maganar cigaba da bunkasar Najeriya ce, a shirye nake. Zan iya ganawa da shi," in ji shi.
Martani kan jita-jitar zai tafi ADC
Dangane da hotunan da suka yadu a kafafen sada zumunta da ke danganta shi da jam’iyyar ADC, Lamido ya ce duk kirkirarrun labarai ne na yanar gizo.
“A wannan zamani na kafafen sada zumunta, komai na iya faruwa. Mutane na zama su kirkiri labarai. Ban ma ga irin wadannan hotuna ba," in ji Sule Lamido

Source: Facebook
Tsohon gwamnan ya kuma jaddada cewa dole ne ‘yan Najeriya su dauki alhakin zaben shugabanninsu, yana mai cewa sakamakon shugabanci yana nuna irin zabin da jama’a suka yi.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya kawo zaman lafiya, kwanciyar hankali da cigaba a Najeriya tare da shiryar da shugabanni su yi abin da ya dace.
Wani dan a mutun PDP a jihar Katsina, Rabiu Kabir, ya shaidawa Legit Hausa cewa suna bukatar duk wanda ke da shakku a kan jam'iyyar ya kama gabansa.
Ya bayyana Sule Lamido a matsayin daya daga cikin iyayen PDP, wadanda daga baya suka rikida suka koma masu cin amamar yayansu.
"Lamido babban kusa ne a PDP, amma yadda ya koma yana yakar jam'iyyar a kotu abin damuwa ne.
"Na dauka yadda aka dauko hanyar gyara da korar baragurbi, zai goya mana baya, ashe shi ma son ransa zai bi, to idan APC yake son shiga ga fili nan ga mai doki," in ji shi.
Sule Lamido ya yi barazanar barin PDP
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido ya bayyana cewa da yiwuwar ya tattara kayansa ya bar jam'iyyar PDP kafin zaben 2027.
Lamido ya bayyana cewa zai iya raba gari da jam'iyyar PDP idan har ba a samu mafita ga rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar ba.
Tsohon gwamnan, wanda yana daga cikin manyan jiga-jigan adawa a Najeriya, ya ce halin da PDP ke ciki a yanzu yana da matuƙar tayar da hankali.
Asali: Legit.ng


