Magana Ta Fito, An Samu Karin Gwamnan PDP da Yan Majalisa da Za Su Koma APC
- Alamu na nuna cewa nan ba da dadewa ba jam'iyyar APC mai-ci a kasa za ta karbi Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri
- Rahotanni sun nuna cewa Gwamna Fintiri da 'yan Majalisar Adamawa na shirin sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulki
- Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyarar aiki Adamawa, inda ya kaddamar da ayyuka
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Adamawa, Nigeria - Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, na shirin bin sahun wasu gwamnonin PDP wajen sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki watau APC.
Majiyoyi da ke da masaniya kan lamarin sun bayyana cewa Gwamna Fintiri tare da ’yan majalisun tarayya da na jiha sun gana kan shirin canza sheka a siyasance.

Source: Twitter
Premium Times ta tattaro cewa gwamna da yan majalisa sun nemi shawarwari daga masu ruwa da tsaki yayin da suke kokarin kammala shirye-shiryen komawa APC.
Gwamna Fintiri ya gana da jagororin APC
A ranar Asabar da ta gabata, Gwamna Fintiri ya karbi bakuncin tawagar jam’iyyar APC karkashin jagorancin shugaban shiyyar Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu a gidan gwamnatinsa da ke Yola.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnan da shugabannin APC sun ci abincin buda baki a gidan gwamnati da ke Yola, lamarin da ya kara rura wutar jita-jitar zai bar PDP.
Taron, wanda ya hada da mambobin majalisar zartarwa ta jihar Adamawa, an gudanar da shi ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin shirin Fintiri na ficewa daga PDP.
Dalilin buda bakin Gwamna Fintiri da 'yan APC
Sai dai, Gwamna Fintiri ya ce an shirya taron buda bakin ne domin karfafa zumunci tsakanin jam’iyyu daban-daban.
Gwamnan ya bayyana cewa:
"Buda baki tare a watan Ramadan yana karfafa zumunci, zurfafa hadin kai, da kuma jaddada kudurinmu na samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali, da ci gaba mai dorewa a jihar Adamawa."
A daidai lokacin da ake yada wannan jita-jita, wani faifan bidiyo da ya karade shafukar sada zumunta ya nuna gwamnan yana jawabi ga dimbin magoya bayansa.
Gwamna Fintiri ya cika baki a siyasar Adamawa
A cikin jawabinsa, Gwamna Fintiri ya jaddada karfin da yake da shi a siyasa, inda ya bayyana cewa yana tare da sanatoci uku, 'yan majalisar wakilai biyar, 'yan majalisar jiha 16, da duka shugabannin kananan hukumomi 21.
Haka zalika, gwamnan ya yi ikirarin cewa yana samun cikakken goyon bayan majalisar zartarwarsa da manyan jami’an gwamnati.

Source: Facebook
Da yake kalubalantar masu sukarsa wadanda bai ambaci sunayensu ba, Gwamna Fintiri ya ce:
"Ina da mataimakin gwamna, sanatoci, wakilai, da shugabannin kananan hukumomi. Ku me ku ke da shi?"
Shirin sauya shekar na gwamnan ya biyo bayan ziyarar da Shugaba Bola Tinubu ya kai jihar kwanan nan don kaddamar da ayyuka.
A yayin ziyarar, shugaba Tinubu ya yaba da kokarin gwamnan, inda ya nuna cewa ayyukansa sun kawo sauyi na zahiri, kamar yadda The Nation ta kawo.
Gwamnan Adamawa zai tura dalibai karatu
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin jihar Adamawa ta amince da daukar nauyin dalibai 100 ‘yan asalin jihar su yi karatun digirin PhD a kasar Turkiyya.
Hakan na zuwa ne bayan taron majalisar zartarwa ta jihar karo na 22 da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Yola, babban birnin jihar Adamawa.
Shirin tallafin karatun na cikin kokarin gwamna Fintiri na bunkasa ilimi da gina hazikan matasa da za su kara wa jihar ma’aikata a fannoni masu muhimmanci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


