2027: Amaechi Ya Sha Sabon Alwashi kan Takarar Shugaban Kasa karkashin ADC
- 'Yan siyasan da ke da burin tsayawa takarar shugaban kasa a 2027, na ta shirye-shirye don ganin sun cimma burinsu
- Rotimi Amaechi wanda yake jigo ne a jam'iyyar ADC, ya bayyana cewa burinsa yana nan na zama shugaban kasa
- Tsohon ministan sufurin ya nuna cewa lokaci ya kurewa gwamnatin Bola Tinubu, domin ta jefa 'yan Najeriya cikin mawuyacin hali
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Rivers kuma babban jigo a jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya yi magana kan burinsa na yin takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Rotimi Amaechi ya bayyana cewa ba gudu ba ja da baya, a yunkurinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2027 karkashin inuwar jam’iyyar ADC

Source: Facebook
Tsohon ministan sufurin ya yi wannan bayani ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Kano, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan
"Na hakura": Gwamna Bala ya bayyana dalilin jingine burin yin takarar shugaban kasa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rotimi Amaechi ya yi wani taro ne da wata hadaddiyar kungiyar ’yan kasuwa ta jihar.
Me Amaechi ya ce kan takara a ADC?
Ya jaddada cewa dole ne zaben fidda gwani na ADC ya kasance an ba kowa dama, inda ya kara da cewa ba zai janye wa kowanne ɗan takara ba, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
"Zan tsaya takarar fitar da gwani na shugaban kasa a jam’iyyar ADC, kuma da ikon Allah, ina fatan na yi nasara domin na fuskanci Tinubu a 2027.”
"Ba zan janye wa kowa ba. A bari al’umma su yanke shawarar wanda suke so ya jagorance su.”
- Rotimi Amaechi
Amaechi ya soki gwamnatin Tinubu
Dangane da halin da kasar nan ke ciki karkashin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Amaechi ya yi suka ga gwamnati, yana mai cewa ’yan Najeriya ba su gamsu da manufofinta da irin salon mulkinta ba.
"Ko gwamnati tana son shirya sahihin zaɓe ko akasin haka, abu ɗaya tabbatacce ne, lokaci ya kure musu. ’Yan Najeriya sun gaji domin babu wanda yake farin ciki a karkashin Tinubu, ko a Rivers ko a Kudancin Najeriya gaba ɗaya."
"Yana ƙoƙarin nuna kamar takaddama ce ta Arewa da Kudu, amma gaskiyar magana ita ce, mutane na cikin wahala a ko’ina."
- Rotimi Amaechi

Source: Twitter
Da aka tambaye shi ko jam’iyyar ADC za ta iya yin tsarin kai tikitin shugaban kasa zuwa Kudu kamar yadda APC da PDP suka yi, Amaechi ya ce:
"Hakan shawarar jam’iyya ce. Ni dai mamba ne kawai. Duk abin da jam’iyyar ta yanke, zan bi. Amma dai abin da na sani shi ne ina cikin 'yan takara."
Amaechi ya yi alkawarin yakar cin hanci
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya sha alwashin kawar da cin hanci da rashawa idan ya zama shugaban kasa.
Amaechi ya bayyana cewa zai yi murabus daga kan mukaminsa, idan ya gaza kawar da cin hanci a cikin wata daya kacal.
Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya nuna cewa zai kuma yi amfani da kudin da aka samu wajen cire tallafin man fetur, zuwa fannin samar da ababen more rayuwa.
Asali: Legit.ng
