Jam'iyyar APC Ta Jawo Ra'ayin Wani Gwamna Zai Koma Cikinta? Gaskiya Ta Bayyana

Jam'iyyar APC Ta Jawo Ra'ayin Wani Gwamna Zai Koma Cikinta? Gaskiya Ta Bayyana

  • Jam’iyyar LP ta tabbatar cewa Gwamna Alex Otti na Abia ba shi da wani shiri na barin inuwarta zuwa APC gabanin babban zaɓen 2027
  • Rahotanni sun nuna gwamnonin hamayya biyar, ciki har da Alex Otti, na shirin komawa APC, amma LP ta ce wannan labari ba gaskiya ba ne
  • Kakakin LP na ƙasa, Obiora Ifoh ya ce suna da kyakkyawar alaƙa da Gwamna Otti kuma ya ba su tabbacin babu inda zai je duk da rade-radin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Abia - Jam'iyyar LP ta ƙasa ta musanta rahoton da ke yawo cewa gwamnan jihar Abia, Alex Otti na shirin sauya sheƙa zuwa APC gabanin zaɓen 2027.

LP ta tabbatar da cewa Gwamna Alex Otti ba shi da wani shiri na komawa jam’iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon tsari, za ta riƙa biyan mutane kudi don su halarci makarantu 2

Gwamna Alex Otti.
Jam'iyyar LP ta musanta jita-jitar da ake cewa Gwamna Alex Otti na shirin sauya sheka zuwa APC Hoto: Alex C. Otti
Asali: Facebook

Sakataren yaɗa labarai na LP ta ƙasa, Mista Obiora Ifoh, ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ranar Juma’a a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana tsoron gwamnoni 5 za su koma APC

Vanguard tace jita-jita ta bazu cewa wasu gwamnonin jam’iyyun hamayya biyar da ke kan wa’adin farko sun shirya shiga APC domin shirya neman tazarce a 2027.

Rahotannin da wasu kafofin watsa labarai suka wallafa sun ce gwamnonin sun haɗa da Alex Otti na Abia, Peter Mba na Enugu da Sheriff Oborevwori na Delta.

Sauran gwamnonin su ne Siminalayi Fubara na jihar Ribas da Fasto Umoh Eno na jihar Akwa Ibom, kamar yadda Daily Post ta kawo.

Gwamna Mba, Fubara, Eno, da Oborevwori ƴan PDP ne yayin da Gwamna Otti kuma ɗan LP ne kuma duka jam’iyyun biyu na fuskantar rikicin cikin gida bayan zaɓen 2023.

LP ta musanta batun sauya shekar Gwamna Otti

Kara karanta wannan

APC ta yi martani bayan El Rufa'i ya kwance mata zani a kasuwa

Da yake zantawa da manema labarai, kakakin LP na kasa ya cire gwamnan Abia daga cikin jerin, ya ce ba shi da niyyar komawa APC.

Obiora Ifoh ya tabbatar da cewa rahoton da ke nuna Otti zai koma APC gabanin 2027 ba gaskiya ba ne, ƙarya ce da wasu bara gurbi suka ƙirƙiro.

“Jita-jita ce kawai ba wani abu ba, mu a jam’iyyar LP muna da kyakkyawar alaka da gwamnanmu, Dr Alex Otti, kuma ya tabbatar mana cewa ba zai tafi ko ina ba gabanin 2027.
“Muna da yakinin cewa zai ci gaba da kasancewa tare da mu, duk da wasu matsalolin da muke ƙoƙarin warwarewa,” in ji shi.

Gwamna Otti na nan daram a jam'iyyar LP

A cewarsa, duk da ficewa daga jam’iyya zuwa wata ba sabon abu ba ne a tsarin dimokuraɗiyya, amma Gwamna Otti ba ya tunanin haɗewa APC mai mulki.

“Kotuna sun sha bayyana fassarar sashe na 84 na kundin tsarin mulki na 1999, kuma mutane da dama da suka taba sauya sheƙa a baya sun fuskanci ƙalubale a kotu.

Kara karanta wannan

APC ta yi kaca kaca da Atiku Abubakar, ta fadi wanda ke haddasa rikici a PDP

“Don haka, idan gwamnonin biyar suna shirin sauya sheƙa, ba sabon abu ba ne, domin hakan ya taba faruwa a baya,” in ji shi.

Dubannin ƴan siyasa sun koma APC

Ku na da labarin Sanata Orji Uzor Kalu ya girgiza ƴan adawa a jihar Abia da ya tarbi mutane sama da 8,000 da suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Orji Kalu ya ce yana aiki tukuri ba tare ba rana domin haɗa kan ƴaƴan APC da nufin karɓe mulkin Abia a zaɓen 2027.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262