Zulum Ya Nuna Gwamna 1 a Arewa, Ya Ce Ya Cancanci Mutane Su Zaɓe Shi a 2027

Zulum Ya Nuna Gwamna 1 a Arewa, Ya Ce Ya Cancanci Mutane Su Zaɓe Shi a 2027

  • Gwamna Babagana Umaru Zulum ya yabawa takwaransa na jihar Kebbi, Nasir Idris bisa ayyukan alherin da yake yi wa al'umma
  • Farfesa Zulum ya ce Dr Nasir Idris Kauran Gwandu ya cancanci ci gaba da zama a kujera lamba ɗaya ta jihar Kebbi har bayan 2027
  • Ya shawarci mazauna Kebbi su rungumi zaman lafiya da haɗin kai kana su ci gaba da marawa nagartaccen gwamnansu baya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kebbi - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum ya nuna gamsuwa da ayyukan aherin da takwaransa na jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris ke yi.

Gwamna Babagana Zulum ya bayyana cewa babu wuri a fadar gwamnatin jihar Kebbi ma'ana Dr. Nasir Idris ya cancanci tazarce a kan madafun iko a 2027.

Gwamna Zulum da Nasir Idris.
Gwamna Zulum ya yabawa takawaransa na jihar Kebbi, ya bukaci al'umma su mara masa baya Hoto: Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu
Source: Facebook

Farfesa Zulum ya bayyana haka ne a Birnin Kebbi a taron kaddamar da wani littafi mai suna 'Sarkin aiki', wanda aka rubuta domin karrama Gwamna Nasiru Idris.

Kara karanta wannan

'Ba mulkin soja ake ba,' Gwamna ya yi kalamai masu zafi ga Tinubu kan kudirin haraji

Gwamna Zulum ya faɗi tushen da ke hana ci gaba

Babagana Zulum ya jaddada cewa zaman lafiya da tsaro su ne ginshikan da sai da su ake samun ci gaba da walwala, kamar yadda Tribune Nigeria ta rahoto.

Gwamnan Borno ya yi kira ga mutanen Kebbi da su hada kai, zauna lafiya, kuma su ci gaba da mara wa Gwamna Nasiru Idris goyon baya domin ya samu damar ci gaba da zuba ayyukan alheri da yake yi.

“Gwamnan ku yana da tawali’u, mutunci, da karimci, na zo nan jihar Kebbi ne saboda nagartarsa.
"Na kaddamar da ayyukan da dan uwana Nasiru Idris ya aiwatar, Kebbi ta samu gagarumin ci gaba a karkashin jagorancinsa."

An kadammar da sabon litttafi

Daga ƙarshe, Farfesa Zulum ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 50 don kaddamar da littafin.

Sakataren APC na kasa, Suleiman Muhammad Argungu, wanda ya wakilci babban mai kaddamarwa ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu, ya yabawa Kauran Gwandu.

Kara karanta wannan

"Mun rasa uwa ta gari," Abba Kabir ya ce bayan rasuwar mahaifiyar gwamna

Ya kara da cewa Sanata Bagudu, wanda bai samu zuwa ba saboda ya tafi wani aiki a birnin Riyadh na kasar Saudiyya, ya bada Naira miliyan 50, yayin da Argungu da kansa ya ba da miliyan 10.

Gwamna Nasir ya rabawa ma'aikata babura

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Kebbi ya rabawa ma'aikatan gidan gwamnati babura domin saukaƙa masu wajen zuwa aiki.

Kwamishinan ayyuka na musamman ya ce akalla ma'aikata 50 ne aka ba baburan a wannan karon domin kara masu kwarin guiwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262