Sabuwar Rigima: 'Dan Takarar Gwamnan PDP na Barazanar Maka Shugaban APC a Kotu

Sabuwar Rigima: 'Dan Takarar Gwamnan PDP na Barazanar Maka Shugaban APC a Kotu

  • Asue Ighodalo ya yi barazanar maka Jarrett Tenebe a kotu saboda zargin da ya yi masa na satar biliyoyin Naira a wani bidiyo
  • An ce Gwamna Monday Okpebholo ya yi kuskuren karanta kasafin kudi, abin da ya jawo Tenebe ya zargi Ighodalo da sata
  • Ighodalo ya nemi Tenebe ta ya bayar da hakuri a fili cikin kwanaki bakwai tare da janye kalaman batanci da ake tuhumarsu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo - Dan takarar gwamna na PDP a zaben Edo, Asue Ighodalo, ya yi barazanar maka shugaban APC, Jarrett Tenebe, a kotu kan batanci.

Ighodalo ya tuhumi Tenebe da yin kalamai marasa tushe da suka bata masa suna ta cikin wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta.

Dan takarar PDP ya yi magana yayin da shugaban APC ya zarge shi da satar kudi
Dan takarar PDP a Edo ya shirya yin karar shugaban APC kan zargin batanci. Hoto: @Aighodalo
Asali: Twitter

Abin da ya hada Ighodalo da shugaban APC

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun fara gwajin bama bamai a Zamfara, yaran Bello Turji sun mutu

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa shugaban APC, Tenebe ya yi zargin cewa dan takarar PDP, Ighodalo ya saci biliyoyin Naira.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tenebe ya yi wannan ikirarin ne yayin martani kan kuskuren Gwamna Monday Okpebholo lokacin gabatar da kasafin kudin 2025.

Legit Hausa ta rahoto Gwamna Okpebholo ya kasa karanta jimillar kasafin kudin yayin da yake gabatar da shi a gaban majalisar dokokin jihar.

Dan takarar ya ba shugaban APC wa'adi

Wannan kuskure na gwamna ya bazu a kafafen sada zumunta, inda mutane da yawa suka yi tsokaci daban-daban kan al’amarin.

Kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito, shugaban APC, Tenebe ya yi martani kan kuskuren gwamnan yana mai cewa:

“Obaseki ba zai yi irin wannan kuskuren ba saboda ya taba sace biliyoyin kudi a baya. Asue Ighodalo ba zai yi irin wannan kuskuren ba saboda ya sace biliyoyi a baya...”

Ighodalo ya ba Tenebe wa’adin kwanaki bakwai don janye kalamansa, bayar da hakuri a fili, tare da tabbacin kada ya sake irin wannan.

Kara karanta wannan

Na farko a Arewa: Gwamna ya gabatar da kasafin kudin Naira tiriliyan 1.5

Majalisa ta yi maganar kujerar Sanata

A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar dattawa ta ayyana kujerar Monday Okpebholo a matsayin wacce babu kowa a kanta bayan zama gwamnan Edo.

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya bukatar hukumar INEC da ya gudanar da zaben maye gurbin kujerar Sanata Okpebholo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.