2027: Atiku Ya Fadi Dalilin Haduwarsa da Peter Obi yayin da Ake Hasashen Haɗaka
- Hadimin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi magana kan ganawar mai gidansa da Peter Obi
- Paul Ibe ya ƙaryata labarin cewa Atiku ya gana da Obi ne saboda zaben 2027 da ake ta hasashen yin haɗaka
- Hakan ya biyo bayan karbar bakuncin Peter Obi da Atiku ya yi a gidansa da ke jihar Adamawa a jiya Asabar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - A jiya Asabar 30 ga watan Nuwambar 2024 aka yi yada cewa Atiku Abubakar da Peter Obi sun gana kan zaben 2027.
Sai dai duka bangarorin biyu sun musanta labarin inda suka ce ganawar ba ta da alaka da zaben 2027.
Atiku ya gana da Peter Obi a gidansa
Hadimin Atiku a bangaren sadarwa, Paul Ibe shi ya ƙaryata labarin inda ya ce haduwa ce ta tsofaffin abokai biyu, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan Atiku ya karbi bakuncin Peter Obi a jiya Asabar 30 ga watan Nuwambar 2024 a gidansa da ke jihar Adamawa.
Atiku ya wallafa wani faifan bidiyo a shafinsa na Facebook inda ya ke tarbar Obi da safiyar jiya Asabar.
Ganawar da manyan yan takarar shugaban kasar suka yi ya sanya shakku inda ake ganin hakan bai rasa nasaba da haɗaka kan zaben 2027.
Atiku ya magantu kan ganawarsa da Obi
"Ka da mu yanke hukunci, Obi ya amince ya yi jawabi a bikin cika shekaru 20 na Jami'ar AUN da ke jihar Adamawa."
"Atiku wanda ya karbi Obi shi ne ya assasa jami'ar, amma mutane suna danganta lamarin da siyasa, kowa ya san abokai ne."
"Atiku ya gayyace shi karin kumallo inda daga nan suka wuce wurin taron, wannan shi ne abin da ta faru."
- Paul Ibe
Yadda Atiku, Obi ke shirin kifar da Tinubu
Kun ji cewa Shugaban kungiyar 'Citizens Coalition' a Najeriya ya yi magana kan hadakar jam'iyyun adawa a zaben 2027.
Shugaban kungiyar, Kelly Agaba ya ce tabbas akwai haske kan tafiyar da ake yi na jam'iyyun adawa da kuma kungiyoyi.
Agaba ya tabbatar da cewa a yanzu haka akwai gwamnoni 15 da suka shiga tafiyar da wasu masu ruwa da tsaki a APC a Arewa.
Asali: Legit.ng