Rikicin APC: Kotu Ta Fatattaki Shugabannin da Ganduje Ya Naɗa
- Rikicin APC ya kara ƙamari a jihar Benue yayin da wata kotu ta fatattaki shugabannin riko da Abdullahi Ganduje ya naɗa
- A ranar 21 ga watan Agusta shugaban APC, Dr. Ganduje ya naɗa shugabannin saboda rikicin siyasa da jam'iyyar ke fama da shi
- A dalilin haka, shugaban da aka dakatar ya shigar kara a kotu domin kalubalantar hukuncin da Ganduje ya yi a watan Agusta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Benue - Rikicin APC a jihar Benue ya kara ɗaukar sabon salo yayin da kotu ta fatattaki shugabannin riko.
Austin Agada ne ke ikirarin jagorantar jam'iyyar APC a Benue kafin Abdullahi Ganduje ya kafa kwamitin rikon.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mai shari'a Tertsea Kume ya rusa kwamitin riƙon bisa laifin karya doka wajen kafa shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An fatattaki shugabannin APC a jihar Benue
Shugaban APC da aka dakatar a jihar Benue, Austin Agada ya shigar da uwar jam'iyyar kara a gaban kotu.
A ranar Alhamis, mai shari'a Tertsea Kume ya saurari karar kuma ya rusa hukuncin da APC ta yi na kafa kwamitin riko a jihar Benue.
Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ne ya kafa kwamitin a ranar 21 ga Agusta domin su yi wata shida kafin a samu damar magance rikicin jam'iyyar.
"Ko Ubangiji da ya halicci sama sa kasa, ya ba mutane mulki a duniya, idan aka masa laifi yana sauraron mutane.
Da Annabi Adamu ya ci dan itace a Aljanna, ba a kore shi a cikinta ba sai da aka tambaye shi dalili.
Amma uwar jam'iyyar APC ta ƙi sauraron shugaban da ta dakatar, sai ta rusa shugabancinsa ba bisa ka'ida ba."
- Mai shari'a Tertsea Kume
Bayan rusa kwamitin da Ganduje ya naɗa, alkalin kotun ya ce duk hukuncin da yan kwamitin suka yi ma ya rushe.
Vanguard ta ruwaito cewa shugaban kwamitin da aka rusa, Benjamin Omale ya ce za su daukaka kara.
Rikicin APC ya shafi sarauta a Sokoto
A wani rahoton, kun ji cewa rikicin cikin gida da ya ɓarke a APC reshen jihar Sakkwato ya fara raba kawunan manyan jiga-jigai da sarakuna.
An ruwaito cewa hakimin Sabon Birni, Alhaji Abdullahi Muhammad Bawa ya yi murabus daga sarauta saboda barin tsagin Sanata Wamakko.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng