Kalubale 4 da Kananan Hukumomi 774 Za Su Fuskanta bayan Samun Gashin Kai

Kalubale 4 da Kananan Hukumomi 774 Za Su Fuskanta bayan Samun Gashin Kai

  • Kananan hukumomi suna farin ciki kotun koli ta yi hukuncin da zai ba su cikakken ‘yanci da cin gashin kai
  • Bincike ya nuna cewa hukuncin bai nufin rayuwar kananan hukumomin za su canza farat daya a Najeriya
  • Akwai wasu matsalolin da ake ganin za a iya tunkara tun daga rikicin doka zuwa kwarewa da sanin makaman aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Kotun koli ta zartar da hukunci cewa dole a rika turawa kananun hukumomi kai-tsaye ba tare da bin ta hannun jihohi ba.

Wannan hukunci ya kawo karshen cin gashin kan da aka dade ana fafutuka a kai, an fara murna cewa kananan hukumomi sun tsira.

Zabe.
Dole a rika yin zaben kananan hukumomi a yanzu Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Kananan hukumomi za su bar hannun gwamnoni

Kara karanta wannan

Ciyamomin ƙananan hukumomi 3 a Arewa sun gamu da hatsari da babura yayin zuwa ofis

Wani bincike da cibiyar Athena ta gudanar kuma ta fitar da bayani a shafinta na yanar gizo ya nuna har yanzu akwai rina a kaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Samun ‘yancin da kananan hukumomin Najeriya suka yi bai nufin nan da ‘yan kwanaki kadan za a ga cigaba a kauyuka da karkara.

Akwai masu ganin cewa rike kudin kananan hukumomi da gwamnoni su ke yi, shi ne ya hana kauyukan kasar nan samun cigaba.

Akwai matsala a wasu kananan hukumomi

Aliyu Isa Aliyu shi ne shugaban hukumar kiddiga ta Kano, ya fara nusar da jama’a cewa wasu kananan hukumomin ba su nuna ba.

A shafinsa na Facebook ya bayyana cewa dole sai an tallafawa wasu kananan hukumomin wajen biyan albashi da sauran ayyuka.

Matsalolin da ke jiran kananan hukumomi

1. Rashin sanin makaman aiki

Ana yawan kukan cewa babu inda ake fama da karancin ma’aikatan da suka san aiki kamar kananan hukumomin da ke jihohin kasar nan.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukunci kasa da awanni 24 kafin zaben Ciyamomi a jihar Kano

Ana bukatar kwarewa a bangarorin kiwon lafiya, kimiyya, noma, ilmi da makamantansu domin dukiyar su ta yi tasiri sosai.

Idan ba a horas da ma’aikatan kananan hukumomi da kyau ba, masana su na ganin zai zama ga kudi ne amma ba a san yadda za batar ba.

2. Cin hanci da rashawa

Babu masu sa ido sosai wajen ganin yadda kananan hukumomi suke gudanar da sha’aninsu, wannan zai iya kawo rashin gaskiya a aiki.

Dole a tashi-tsaye domin tabbatar da cewa ba a karkatar da dukiyoyin al’umma ba idan ana son cigaban da ake tunani a kananun hukumomi.

Hukumomin EFCC, ICPC, NFIU, CCB da CCT sun maida hankali a kan manyan ma’aikata, watakila ba dole ba ne su iya baza ido a ko ina ba.

3. Rashin gudanar da zabe mai kyau

Labaran da ake gani yau da kullum sun nuna akwai alamar tambaya game da irin zaben kananan hukumomin da ake gudanarwa a yau.

Kara karanta wannan

‘Za a yi aikin banza’: Lauya ya kawo shawara da kotu ta hana zaben jihar Kano

A maimakon INEC, hukumomin jiha ne suke shirya zabukan kuma ana zargin gwamnoni ne suke ba da takara ga wadanda suka so.

Mafita ita ce a gyara harkar zaben kananan hukumomi domin rage magudi. Gwamnatin Nasir El-Rufai ta kamanta hakan a 2021.

4. Rudani a tsarin mulki

Kamar yadda ake shirya zabe, duk da an ba kananan hukumomin ‘yancin kashe kudinsu, ana bukatar doka ta fayyace matsayin kowa da kyau.

Muddin ba a yi wannan ba, za a cigaba da zargin gwamnonin jihohi da yi wa kananan hukumominsu katsalandan kamar yadda aka saba ji.

Ana ganin yadda gwamnan Anambra ya fito da wata doka wanda za ta ba jiha damar tatsar kudi daga cikin asusun kananan hukumomi.

Ayyuka a kananan hukumomin Kano

Kwanaki aka ji labari mutanen yankunan Rogo, Albasu, Kibiya, Garko, Kura da Madobi za su amfana da ayyukan N28bn a Kano.

Yawanci ma’aikatar ayyuka da harkar ilmi za su yi wadannan kwangiloli, wasu kuma ana tsakiyar yin su a yanzu a gwamnatin NNPP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng