Mohammed Yayari: Dalilin Naɗa Sabon Shugaban Jam'iyyar PDP na Ƙasa Ya Bayyana

Mohammed Yayari: Dalilin Naɗa Sabon Shugaban Jam'iyyar PDP na Ƙasa Ya Bayyana

  • Yayin da rikici ke ƙara dagula babbar jam'iyyar adawa, Mohammed Yayari ya yi magana bayan naɗa shi shugaban tsagin PDP
  • A wata sanarwa da ya fitar, sabon shugaban PDP na riƙon kwarya ya ce an naɗa shi ne domin dawo da jam'iyyar kan ganiyarta
  • Ya ce zai yi aiki tukuru a tare da kaucewa kundin tsarin mulki ba wajen haɗa kan ƴaƴan PDP da warware duk wsta sarƙaƙiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Sabon muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Mohammed Yayari ya ce an naɗa shi wannan muƙami ne domin dawo da martabar jam"iyyar.

Mohammed ya yi wannan furucin ne a takardar karɓar muƙamin shugaban PDP na rikon ƙwarya wanda za a iya cewa tsagi ɗaya na jam'iyyar ya naɗa shi.

Kara karanta wannan

2027: Tsohon gwamnan PDP ya shawarci Atiku ya hakura da takara, ya fadi dalili

Mohammed Yayari.
Muƙaddashin shugaban tsagin PDP, Mohammed Yayari ya faɗi dalilin naɗa shi a muƙamin Hoto: Mohammed Yayari
Asali: Facebook

Mohammed Yayari ya ɗauki alƙawari a PDP

Ya kuma yi alkawarin yin aiki tukuru don sake farfado da kwarin gwiwa da burin ƴan jam’iyyar tare da hada kan kwamitin gudanarwa NWC na ƙasa, rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sabon shugaban tsagin jam'iyyar PDP ya kara da godewa ƴan kwamitin NWC da sauran ƴaƴan jam'iyya bisa yadda suka nuna jajircewa wajen ganin PDP ta yunƙuro ɗa ƙarfinta.

Yayari ya tabbatar da cewa a ƙarkashin jagorancisa, NWC zai yi aiki tuƙuru ba tare da ƙetare tanadin kundin tsarin mulkin PDP ba.

Tsohon ma’ajin jam’iyyar na kasa ya kara da cewa zai yi adalci ga dukkan ‘ya’yan PDP ba tare da la’akari da matsayinsu ko jihar da suka fito ba, Vanguard ta ruwaito.

Dalilin naɗa shugaban tsagin jam'iyyar PDP

Mohammed Yayari ya ce:

"A ƙoƙarin dawo da jam'iyyar kan turba, kwamitin NWC ya naɗa ni a matsayin muƙaddashin shugaban jam'iyya na ƙasa a ranar Alhamis, 10 ga watan Oktoba, 2024.

Kara karanta wannan

Sukar Tinubu: Kalaman sanatan APC na neman kara sanya shi cikin matsala

"An ba ni wannan dama ne domin na jagoranci aikin farfaɗo da jam'iyyar ta dawo kan ganiyarta kamar yadda matasa da sauran masu ruwa da tsaki ke buri."

Rikicin PDP: Fayose ya ba Atiku shawara

A wani labarin kun ji cewa tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, ya yi magana kan babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara

Ayo Fayose ya buƙaci Atiku Abubakar da ya haƙura da sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a inuwar PD0 a zaɓe mai zuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262