Ondo 2024: APC Ta Samu Matsala Ana Shirin Zabe, Mutane 1200 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP

Ondo 2024: APC Ta Samu Matsala Ana Shirin Zabe, Mutane 1200 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP

  • Rahotanni sun bayyana cewa kimanin 'ya'yan jam'iyya mai mulki ta APC a jihar Ondo ne suka sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta PDP
  • An ruwaito cewa tsohon mai neman takarar kujerar sanata mai wakiltar shiyyar, Dakta Adeniran Oyebade ne ya jagoranci mutanen
  • Dan takarar gwamnan Ondo karkashin PDP, Agboola Ajayi wanda ya karbi masu sauya shekar, ya sha alwashin yin aiki idan aka zabe shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ondo - Kimanin 'yan jam'iyyar APC daga kananan hukumomi shida na mazabar Ondo ta tsakiya a majalisar dattawa suka sauya sheka zuwa PDP.

Tsohon mai neman takarar kujerar sanata mai wakiltar shiyyar, Dakta Adeniran Oyebade ne ya jagoranci dubunnan 'yan APC zuwa PDP.

Kara karanta wannan

Bayan bidiyon Dan Bello, Abba ya rasa goyon bayan tsohon na hannun daman Kwankwaso

Magoya bayan jam'iyyar APC 1200 sun sauya sheka zuwa PDP a Ondo
APC ta yi rashin magoya baya 1200, sun sauya sheka zuwa PDP a Ondo. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ondo: 'Yan APC 1200 sun koma PDP

Jaridar The Nation ta ruwaito Hon. Adeniran, wanda ya yi magana a madadin wadanda suka sauya shekar ya ce zai yi aiki domin ganin PDP ta yi nasara a Nuwamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Adeniran ya jaddada goyon baya da mubayi'a ga dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar adawa ta PDP a jihar, Agboola Ajayi.

Tsohon mai neman takarar ya ce sun gano cewa jam’iyyar APC ba ta da wani shiri na kawo ci gaba ga al’ummar jihar Ondo.

'Dan takarar PDP ya yi maraba

Ya bayyana cewa ya kwashe sama da shekaru tara a jam’iyyar APC kuma ya bayar da gudunmawa sosai ba tare da an saka masa ba.

Da yake karbar wadanda suka sauya shekar, Hon. Ajayi ya ce a shirye yake ya yi wa jama’a hidima idan aka ba su goyon bayan a zaben jihar na Nuwamba.

Kara karanta wannan

Ana fargabar kitsa makarkashiya ga shirin tazarcen shugaba Tinubu a zaben 2027

Dan takarar gwamnan na PDP ya ce yana da dukkan abubuwan da ake bukata domin kai al’amuran jihar zuwa tudun mun tsira.

Ondo 2024: Ajayi ya zama dan takarar PDP

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon mataimakin gwamnan jihar Ondo, Agboola Ajayi, ya zama dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan da za a yi a watan Nuwamba.

A zaben fitar da gwani da PDP ta gudanar, Agboola Ajayi ya samu kuri’u 264, yayin da tsohon dan majalisar wakilai, Hon. Kolade Akinjo wanda ke bin bayansa ya samu kuri'u 157.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.