Zamfara: An Bayyana Wadanda Suke Son Ruguza APC Domin Yiwa Tinubu Illa

Zamfara: An Bayyana Wadanda Suke Son Ruguza APC Domin Yiwa Tinubu Illa

  • Wata kungiya a Arewacin Najeriya ta bayyana dalilin da yasa rikicin jam'iyyar APC yaki ci yaƙi cinyewa a Zamfara
  • Kungiyar ta bayyana yadda neman mukami daga gwamnatin tarayya ke kara rura wutar rikicin jami'yyar a tsakanin shugabanni
  • Shugabannin kungiyar sun ce sabuwar alakar siyasa tsakanin Bello Matawalle da Abdulaziz Yari na daya daga cikin matsalolin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Ana cigaba da sharhi kan rikicin siyasa da ya jawo rabuwar kai a jam'iyyar APC a Zamfara.

Wata kungiya mai rajin wayar da kan al'umma a Arewacin Najeriya (NAN) ta bayyana dalilin kin karewar rikicin.

Bola Tinubu
An bayyana yadda rikicin APC zai shafi Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa kungiyar NAN ta ce akwai masu neman matsayi da suka tayar da hankali kan ganin rikicin ya cigaba.

Kara karanta wannan

Sarkin Ilemona: Dogarin Shugaba Bola Tinubu ya samu babbar sarauta a jihar Kwara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zamfara: Dalilin rikicin APC

Kungiya mai rajin wayar da kai ga al'ummar Arewa (NAN) ta yi ikirarin cewa hadin kan Abdulaziz Yari da Bello Matawalle wajen goyon bayan Tinubu ne ya tayar da hankalin yan APC a Zamfara.

NAN ta ce hakan ne yasa sauran yan siyasa irin Sanata Kabiru Marafa da Sani Jaji suke ƙoƙarin ballewa daga jami'yyar.

Kungiyar NAN ta zargi Sanata Kabiru Marafa da Sani Jaji da kin goyon bayan Bola Tinubu, saboda haka nema a cewarta suka ware gefe.

NAN: 'A binciki tsagin APC a Zamfara'

Har ila yau, kungiyar NAN ta ce Sanata Marafa yana fushi da Tinubu ne saboda rasa muƙamin gwamantin tarayya, rahoton Authority News.

A cewar kungiyar, dan majalisar tarayya, Sani Jaji kuma yana kin Tinubu ne saboda rasa muƙamin kakakin shugaban majalisar dokoki.

Kara karanta wannan

Ka zo a zauna: Jigon PDP ya nemo hanyar sasanta Fubara da Wike, ya sanya Atiku a ciki

Saboda haka kungiyar ta ce ya zama wajibi a binciki yadda suke raba kan jami'yyar domin hakan zai iya yiwa jam'iyyar illa a zabe mai zuwa.

APC ta dakatar da dan majalisa

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta tabbatar da dakatar da ɗan majalisar Kaura Namoda da Birnin Magaji, Honorabul Aminu Sani Jaji a jihar Zamfara.

Sakataren APC na jihar, Alhaji Ibrahim Umar Dangaladima, ya ce kwamitin zartarwa ya amince da rahoton kwamitin ladabtarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng