'Yan Bindiga Sun Fatattaki Mutane Daga Gidajensu a Jihar Neja

'Yan Bindiga Sun Fatattaki Mutane Daga Gidajensu a Jihar Neja

  • Hare-haren yan bindiga ya tilsatawa mutane da dama barin gidajensu a yankunan jihar Neja dake Arewa maso tsakiyar Najeriya
  • Yankunan da abin ya shafa sun hada da Kemaka, Roro, Unguwan Usman, Rumace da Bassa a karamar hukumar Shiroro
  • Kwamishinan tsaro na jihar, Birgediya Janar Bello Abdullahi Muhammad (Mai ritaya) ya bayyana matakin da suka dauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

jihar Neja - Ayyukan yan bindiga sun tilastawa daruruwan mutane guduwa daga gidajensu a yankuna daban-daban na jihar Neja.

Police Ng
Mutane sun bar gidajensu saboda harin yan bindiga a Neja. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Hare-haren 'yan bindiga a Neja

Rahotanni sun nuna cewa yankunan da sababbin hare-haren ya shafa sun hada da Kemaka, Roro da Unguwan Usman.

Kara karanta wannan

Fitattun 'yan Arewa guda 5 da Bola Tinubu ya ba manyan mukamai a jami'o'i

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cikin wani rahoto da jaridar Daily Trust ta wallafa an gano cewa sauran yankunan sun hada da Rumase da kuma Bassa.

Yaushe yan bindiga suka kai harin?

Rahotanni da suka fito daga yankunan sun nuna cewa yan bindigar sun kai hare-haren ne a yankunan a ranar Lahadi da ta wuce.

Hakan ya tilastawa mutanen yankunan barin gidajensu tare da kwana da neman mafaka a cikin dazuka.

Gwamnatin Neja ta tabbatar da lamarin

Gwamnatin jihar Neja tabbatar da faruwar lamarin ta kuma bayyana matakin da za ta dauka cikin gaggawa.

Kwamishinan tsaro na jihar, Birgediya Janar Bello Abdullahi (Mai ritaya) ne ya tabbatar da kai hare-haren wa yan jarida ta wayar tarho.

Matakin da gwamnatin Neja za ta dauka

Kwamishinan ya bayyana cewa a yanzu haka suna ƙoƙarin samar da tsaro a yankunan musamman wuraren da ake noma.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi garkuwa da jami'in kwastam a Abuja

Ya ce suna ƙoƙarin samar da gidaje na wucin gadi da waɗanda suka rasa gidajensu za su zauna na dan lokaci.

A cewarsa an dauki matakin samar da gidajen wucin gadin ne saboda ko da mutanen sun koma garinsu ba za su samu kwanciyar hankali ba.

Yan bindiga sun kai hari a masallaci

A wani rahoton, kun ji cewa rahotanni sun bayyana cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari kan masu ibada a lokacin sallar Tahajjud a wani kauyen Minna.

Mazauna yankin na Neja sun shaida wa manema labarai cewa 'yan bindigar sun kai farmaki da karfe 1 na dare lokacin da za a fara sallar dare.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng