Sanatoci Za Su Kafa Kwamitin Binciken Buhari a Kan Bashin N30tr da Ya Ci aCBN

Sanatoci Za Su Kafa Kwamitin Binciken Buhari a Kan Bashin N30tr da Ya Ci aCBN

  • Majalisar dattawa ta kafa kwamiti da zai binciki abubuwan da suka faru a lokacin Muhammadu Buhari yana kan karagar mulki
  • Sanata Yahaya Abdullahi mai wakiltar Kebbi ta Arewa ya gabatar da rahoton da ya tabo bashin da CBN ya ba gwamnatin Najeriya
  • ‘Yan majalisar sun ce ba su san yadda gwamnatin tarayya ta kashe N30tr ba, saboda haka dole binciki bashin da sauran tsare-tsare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Sanatoci sun kafa wani kwamiti na musamman da zai yi bincike a kan wasu bashi da gwamnatin Muhammadu Buhari ta karbo.

A lokacin Muhammadu Buhari yana ofis, gwamnatin tarayya ta karbi aron N30tr daga CBN, This Day ta ce za a binciki wannan bashi.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta gaji, ta shirya binciken bashin N23tr da Emefiele ya ba gwamnatin Buhari

Buhari
Majalisa za ta binciki Gwamnatin Buhari Hoto: Nigerian Senate/Buhari Sallau
Asali: Facebook

Ganin halin da tattalin arzikin kasa ya shiga, Sanatocin kasar sun zargi gwamnatin da ta wuce da hannu saboda yadda ta rika cin bashi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatoci za su binciki gwamnatin Buhari

‘Yan majalisar sun yanke matsayar ne a wajen tattaunawa game da rahoton kwamitin harkokin banki, inshora, gona, tattali da kasafi.

Shugaban kwamitin, Sanata Yahaya Abdullahi ya gabatar da rahoton da ya zargi yawan cin bashi a matsayin silar lalacewar tattalin arziki.

Sanatan na PDP ya bada shawarar cewa gwamnatin tarayya ta biya bankin CBN bashin N30tr da ta karba domin rage kudin da yake yawo.

Za a binciki tsare-tsaren Emefiele a CBN

Vanguard ta ce an bukaci CBN ya karbo bashin da ya rika ba mutane. Hakan yana nufin za a binciki batun N10tr da aka ba manoma aro.

Kara karanta wannan

Sanatoci sun lalubo yadda Gwamnatin Buhari ta haddasa asarar Naira tiriliyan 17

Majalisar dattawa za ta duba tsare-tsaren tallafin bankin CBN da cinikin $2.4bn da aka yi wajen mu’amala da kudin kasashen ketare.

A karshe jaridar ta ce an yi na’am da kafa kwamiti da zai binciki yadda aka karbi aron kudi a hannun CBN tun da dama a asirce aka yi.

A binciki Shugaba Buhari ko a'a?

Sanatoci kamar Barau Jibrin da Ali Ndume suna zargin ba su san yadda gwamnatin Buhari ta kashe duk bashin kudin da CBN ya bada ba.

Ahmad Lawan wanda shi ne tsohon shugaban majalisar dattawa bai gamsu da wannan ba, yana ganin binciken bai da wani amfani.

Gwamnatin za ta binciki bashin da Buhari ya ci

Gwamnatin Muhammadu Buhari ta bar shugaba Bola Tinubu da biyan bashi, an ji labari Wale Edun ya ce sai sun yi bincike da kyau za a biya.

A sa’ilin da Godwin Emefiele yake rike da CBN aka rika ba Najeriya aron kudin da aka buga daga bankin, wasu sun ce wannan ya tashi kimar Dala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel