Tsohon Minista Ya Zargi Ganduje da Damagun da Jefa Gwamnan PDP a Matsala

Tsohon Minista Ya Zargi Ganduje da Damagun da Jefa Gwamnan PDP a Matsala

  • Dattijo kuma shugaban kungiyar PANDEF ta mutanen Neja Delta, Edwin Clark ya yi martani kan rikicin siyasa a jihar Rivers
  • Clark ya zargi shugabannin manyan jam'iyyun APC da PDP da hannu a cikin rikicin domin tozarta Gwamna Siminalayi Fubara
  • Ya bukaci Abdullahi Ganduje da Umar Damagun da su tsame hannunsu a wannan rikici da ke faruwa a jihar wanda ke kara ƙamari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kungiyar PANDEF a Neja Delta, Edwin Clark ya magantu kan rikici tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Nyesom Wike.

Edwin Clark ya zargi shugabannin jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje da na PDP, Umar Damagun da ruruta wutar rikicin jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Fitattun 'yan Arewa guda 5 da Bola Tinubu ya ba manyan mukamai a jami'o'i

Tsohon Minista ya zargi Ganduje da Damagun kan rikicin Rivers
Dattijo Edwin Clark ya zargi Ganduje da Damagun da hannu a rikicin siyasar Rivers. Hoto: Official Peoples Democratic Party.
Asali: Facebook

Rikicin Rivers: An zargi Ganduje, Damagun

Tsohon ministan ya ce shugabannin jam'iyyun suna hada kai da Nyesom Wike domin kawo cikas ga gwamnatin Fubara, cewar rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dattijon ya bayyana haka ne a cikin wata wasika da ya tura ga Ganduje da Damagun a jiya Litinin 20 ga watan Mayu.

Ya ce Ganduje da Damagun sun san abin da ke faruwa a River tare da goyon bayan Wike da ke juya dukkan jam'iyyun a jihar, cewar Vanguard.

"Ta yaya Gwamnatin Tarayya da manyan jam'iyyun kasar za su bar mutum daya yana cin zarafin zaɓaɓɓen gwamna da cewa shi ya daura shi a mulki ba mutanen Rivers ba."

- Edwin Clark

Rivers: Clark ya gargadi Ganduje da Damagun

Clark ya kuma shawarci shugabannin jam'iyyun biyu da su tsame hannunsu a ruguntsumin siyasar jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan ya tsoma baki kan rigimar Ministan Tinubu da gwamnan PDP

Ya ce jihar tana da matukar muhimmanci a Najeriya wacce take samar da mafi yawan karfin tattalin arzikin kasar.

Gwamna Fubara ya sake dira kan Wike

A wani labarin, an ji Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya caccaki tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike kan yadda ya yi mulki a jihar

Fubara ya bugi kirji kan ayyukan alheri da ya kawo jihar a cikin shekara daya kacal duk da rikicin siyasar jihar.

Gwamnan ya ce ayyukan da ya yi a shekara daya ya fi na gwamnatoci da dama da suka yi shekaru takwas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel