Mata Sun Shiga Tashin Hankali Bayan 'Yan Bindiga Sun Kashe Mazajensu a Neja

Mata Sun Shiga Tashin Hankali Bayan 'Yan Bindiga Sun Kashe Mazajensu a Neja

  • Wata kungiyar matasa a jihar Neja ta arewa ta bayyana halin kunci da mata da yan bindiga suka kashe mazajensu suka shiga
  • Kungiyar ta kuma bayyana cewa sama da yankuna 80 ne yan bindiga suka lalata da korar al'umma a karamar hukumar Mariga
  • Shugaban kungiyar, Sahabi Mamuda ya yi kira na musamman ga ministan harkokin mata kan lamarin da mata ke ciki yau

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Neja - Kungiyoyin matasa a jihar Neja sun bayyana halin da matan da aka kashe masu daukan dawainiyarsu suka shiga.

Gwamnan Neja
Matan da aka kashe mazajensu sun shiga damuwa a jihar Neja. Hoto: Umaru Mohammed Bago
Asali: Facebook

Ta'adin 'yan bindiga a kauyukan jihar Neja

Kungiyar ta bayyana cewa 'yan bindiga sun kashe iyayen mata da dama a kauyuka sama da 80 a yankin Mariga.

Kara karanta wannan

Atiku ya nemi takawa Bola Tinubu burki kan taba kudin ’yan fansho ayi ayyuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton Amiya ya nuna cewa mata daga ƙauyuka daban-daban suna cikin halin kunci kan lamarin rayuwa.

Halin da matan Neja ke ciki

Rahotanni sun tabbatar da cewa a halin da matan ke ciki ba su samu wani tallafin kirki daga gwamnati ba kuma hakan zai iya kai su halaka.

Kungiyar ta ce barazanar da matan ke fuskanta zai iya kai su fadawa ayyukan sabon kamar zina da shaye-shaye domin neman biyan bukatunsu na yau da kullum.

Mata na neman sana'a bayan rasa mazaje

Har ila yau kungiyar ta yi kira ga taimakon matan da jari domin fara sana'o'in da za su rufawa kansu asiri.

Sun ce sun riga sun nuna sha'awar fara sana'a amma babba kalubalen da ya hana su shi ne rashin jari.

Kungiyar ta yi kira ga ministar mata

Shugaban kungiyar, Sahabi Mamuda Auna ya yi kira ga ministan harkokin mata da ta kawo gudunmawa ga matan.

Kara karanta wannan

Hukumar Hisbah ta saka sabuwar doka kan harkokin biki a jihar kano

Malam Sahabi Mamuda ya ce taimakon ne ya kamata ministar ta mayar da hankali a kai maimakon shiga lamarin hana auren marayu da za a yi a jihar.

Halin da garin Mariga ke samu kan shi

Ƙaramar hukumar Mariga tana daga cikin wuraren da ayyukan yan bindiga ya yi tsanani wanda mutane da dama sun gudu sun bar gidajensu.

Hakan ya sanya masu sana'o'i sun rasa ayyukansu ta yadda wasu suka koma bara a wasu wurare na dabam.

An kashe sojoji a jihar Neja

A wani rahoton, kun ji cewa sojoji sun sake tafka babban rashi bayan kisan wasu sojoji shida da 'yan bindiga suka yi a jihar Neja da ke Arewacin Najeriya

Yayin harin da ya yi ajalin sojojin, maharan sun kuma yi garkuwa da wani Kyaftin din soja a kauyen Roro da ke jihar ta Neja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng