Kano: Jami'yyar APC Ta Yi Martani Kan Kiran Tinubu Ya Kori Ganduje, Ta Tona Asirin Kwankwasiyya

Kano: Jami'yyar APC Ta Yi Martani Kan Kiran Tinubu Ya Kori Ganduje, Ta Tona Asirin Kwankwasiyya

  • Jami'yyar adawa ta APC a jihar Kano ta yi martani kan kiraye-kirayen korar shugaban jam'iyyar ta kasa, Dakta Abdullahi Ganduje
  • Mataimakin shugaban jam'iyyar a jihar, Shehu Maigari ya yi fatali da kiraye-kirayen inda ya ce 'yan Kwankwasiyya ne suka dauki nauyinsu
  • Wannan na zuwa ne bayan wasu matasan jam'iyyar APC sun bukaci Tinubu ya kori Ganduje bayan gaza yin nasara a zaben gwamnan jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Jami'yyar APC a jihar Kano ta yi zazzafan martani kan kiran a kori shugaban jam'iyyar, Umar Ganduje.

Jami'yyar adawa a jihar ta ce 'yan Kwankwasiyya ne suka dauki nauyin matasan APC kan wannan kira da a sauke Ganduje.

Kara karanta wannan

Kano: Dattawan APC a jihar sun shawarci Tinubu kan korar Ganduje, sun bayyana matsayarsu

Jami'yyar APC ta yi martani kan kiraye-kirayen korar shugaban jam'iyyar, Ganduje
Jami'yyar APC ta yi fatali da kiraye-kirayen Tinubu ya kori shugaban jam'iyyar, Ganduje. Hoto: Bola Tinubu, Umar Ganduje.
Asali: Facebook

Wane kira matasan suka yi kan korar Ganduje?

Idan ba a mantaba a jiya Lahadi 21 ga watan Janairu wata kungiyar matasa ta bukaci Tinubu ya kori Ganduje daga kan kujerar shugabancin jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasan sun yi wannan kira ne yayin da suke zargin Ganduje da gaza yin nasara a zaben jihar da aka gudanar a watan Maris.

Shugaban kungiyar, Sadiq Ali Sango shi ya yi wannan kira a jiya Lahadi 21 ga watan Janairu a Kano, kamar yadda The Guardian ta tattaro.

Wane martani APC ta yi kan korar Ganduje?

Mataimakin shugaban jam'iyyar a jihar, Shehu Maigari ya yi fatali da kiran inda ya ce matasan ba 'yan APC ba ne.

Maigari ya ce sun sani a APC ba su da matasan da ke kiran haka, kuma shugabanninta sun san masu daukar nauyin irin wadannan, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

A je a sasanta da Kwankwaso: Sirrin taron Ganduje, ‘yan APC da Tinubu sun fito fili

Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin akwai wani shirin hadaka tsakanin Sanata Kwankwaso da jami'yyar APC.

Jita-jitar komawar Kwankwaso APC

Kun ji cewa, Jita-jitar komawar Sanata Rabiu Kwankwaso ta kara tabbata bayan ganinsa da jigon APC, Cif Bisi Akande.

A baya, ana ta rade-radin cewa Sanatan ya yi yarjejeniya da jam'iyyar APC cewa akwai alamun ya koma jam'iyyar inda shi kuma a bangarensa ya musanta zargin.

Wannan na zuwa ne bayan samun nasara a Kotun Koli da Gwamna Abba Kabir ya yi wanda ya kasance dan jam'iyyar NNPP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.