Hajjin 2024: Gwamna Ya Gwangwaje Maniyyata 2,682 da Kyautar $100

Hajjin 2024: Gwamna Ya Gwangwaje Maniyyata 2,682 da Kyautar $100

  • Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya ba da tallafin kudi ga maniyyatan jihar 2,682 da za su tashi zuwa Saudiyya
  • Gwamnan ya ba da kyautar $100 ga kowane maniyyaci a jihar domin ragewa musu halin da suke ciki na tsadar rayuwa
  • Sanata Bala ya bayyana haka ne yayin da yake jawabin bankwana a sansanin aikin hajjin Sultan Sa'ad Abubakar da ke Bauchi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bauchi - Gwamna Bala Mohammed ya gwangwaje maniyyatan jihar Bauchi da kyautar makudan kuɗi.

Gwamnan ya ba dukkan maniyyatan jihar 2,682 kyautar $100 domin tallafa musu yayin da suke kasa mai tsarki.

Gwamna ya ba maniyyatan jiharsa kyautar $100
Sanata Bala Mohammed ya gwangwaje maniyyatan Bauchi da kyautar $100 kowannensu. Hoto: Hoto: Bala Mohammed.
Asali: Twitter

Gwamna ya shawarci maniyyatan Bauchi

Kara karanta wannan

Rivers: Gwamna ya kuma ɗaga yatsa ga Wike, ya bugi kirji kan jikkata abokan gaba

Bala ya bayyana haka ne yayin jawabin bankwana ga maniyyatan a sansanin aikin hajji na Sultan Sa'ad Abubakar da ke Bauchi a jiya Juma'a 17 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatan ya bukaci maniyyatan da su kasance jakadun jihar Bauchi nagari dama Najeriya baki daya, cewar rahoton Leadership.

Ya hori maniyyatan da su dage da yi wa Najeriya addu'ar zaman lafiya da kuma ci gaba a halin da ake ciki, kamar yadda Tribune ta tattaro.

Shirin da gwamnan ya yiwa maniyyatan Bauchi

Tsohon ministan ya ce sun yi dukkan mai yiwuwa wurin shirya tarbar maniyyatan karkashin jagorancin Amirul Hajji kuma Sarkin Dass, Usman Bilyaminu.

A martaninsa, Amirul Hajji, Usman Bilyaminu ya yabawa gwamnan kan irin shirye-shiryen da aka yi domin gudanar da aikin hajji cikin sauki da kuma walwala.

Sarkin ya kuma godewa gwamnan kan muƙamin da ya ba shi inda ya ce zai yi kokari wurin inganta harkokin aikin Hajjin bana.

Kara karanta wannan

Jerin tsofaffin gwamnoni da basu ga maciji da yaran gidansu bayan ɗarewa mulki

Tinubu ya saka tallafi a aikin hajji

A wani labarin kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya ba da tallafin N90bn a aikin hajjin bana yayin da kujera ta yi tsada.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima shi ya bayyana haka inda ya ce tallafin zai taimaka wurin ragewa maniyyatan wahala.

Shettima ya ce shugaban ya himmatu wurin inganta tattalin arzikin Najeriya domin samun daidaito a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.