J.I Okoro: Abubuwa 5 Kan Alkalin Kotun Koli da Zai Yanke Hukunci a Shari’ar Abba v APC

J.I Okoro: Abubuwa 5 Kan Alkalin Kotun Koli da Zai Yanke Hukunci a Shari’ar Abba v APC

  • John Inyang Okoro shi ne babban Alkalin da ke jagorantar zaman shari’ar zaben gwamnan jihar Kano a Kotun Koli
  • Alkalin ya dade a babban kotun kasar, shi da wasu abokan aikinsa hudu za su rabawa NNPP da APC gardama
  • Asalin John Inyang Okoro mutumin jihar Akwa Ibom ne, ya yi karatun ilmin shari’arsa ne a 1980s a garin Legas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Mun kawo takaitaccen bayani a kan Mai shari’a John Inyang Okoro

1. Haihuwa

Bayanan da aka samu daga shafinsa na kotun koli sun nuna an haifi John Inyang Okoro ne a ranar 11 ga watan Yuli a 1959.

An haifi Alkalin ne a garin Nung Ukim da ke karamar hukumar Ikono a jihar Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

Sabon rikici zai kurdo jam’iyyar PDP, Atiku ya lula Dubai bayan shari’ar zabe

Kano.
Alkalin zaben Kano, John Inyang Okoro a kotun koli venturesafrica.com
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. Karatu

Alkalin ya fara karatunsa a makarantar Methodist School da ke Nung Ukim, a nan ya yi firamare daga 1965 zuwa 1972.

Tsakanin 1973 zuwa 1977, yana garin Oron, inda ya samu ilminsa na sakandare a makarantar Boys High School.

Daga nan sai ya tafi Uyo domin karatun sharar fagen shiga jami’a tsakanin 1979 da 1981.

Daga shekarar 1981 zuwa 1984, yana jami’ar Legas. Bayan ya gama ya tafi makarantar koyon aikin shari’a 1985 da ke Legas.

3. Aikin shari’a

John Inyang Okoro ya fara aikin shari’a ne a kotun majistare a 1986. Da aka yi shekaru 10 ya zama babban Alkalin majistare.

Bayanan sun nuna daga 1998 zuwa 2006, yana teburin babban kotu a jihar Akwa Ibom, bayan na sai ya tafi kotun daukaka kara.

Bayan shafe shekaru bakwai, John Okoro ya samu karin matsayi zuwa kotun kolin kasa.

Kara karanta wannan

An saurari karar Abba, Kotun Koli za ta yanke hukunci a shari’ar gwamnan Kano

4. Ayyuka na musamman

A 1998, yana cikin alkalan korafin shari’ar zaben Kano, ya yi wannan aiki a zabukan gwamna da majalisa a Delta da Ondo a 2003.

Da aka zabo Alkalan da za su yi hukunci a kan karar zaben shugaban kasa tsakanin Bola Tinubu da PDP da LP, Okoro yana cikinsu.

5. Alkalin kotun koli a hannun DSS

Za a iya tuna cewa a shekarar 2016, Okoro yana cikin alkalan da DSS ta cafke da sunan karbar cin hanci da rashawa da rashin gaskiya.

Bayan an yi bincike, hukumar DSS ta wanke shi daga zargi, kuma ba a kai shi kotu ba.

Shari'ar zaben Kano a kotun koli

Ana da labari Wole Olanipekun ya fadawa kotun koli kuri’un da aka sokewa NNPP sun na halal ne, kuma ba a kotu aka yi aiki a kan su ba.

Shi ma Lauyan NNPP, Adegboyega Awomolo, ya fadawa kotun kolin kasar babu dalilin a azabtar da mutanen Kano saboda kuskuren INEC.

Kara karanta wannan

Atiku, Amaechi, Shekarau, Binani da jiga-jigan ‘yan siyasa da suka fi kowa asara a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel