Atiku, Amaechi, Shekarau, Binani Da Jiga-Jigan ‘Yan Siyasa Da Suka Fi Kowa Asara a 2023

Atiku, Amaechi, Shekarau, Binani Da Jiga-Jigan ‘Yan Siyasa Da Suka Fi Kowa Asara a 2023

Abuja - Fitattun ‘yan siyasa bila-adadin ba su samu yadda su ke a zaben da aka yi a shekarar nan ba, amma akwai wanda rashinsu ya fi zafi.

Rahotonmu ya tattaro jerin ‘yan siyasan da su ka shiga takara ko aka sa ran za su samu mukami a gwamnati, amma su ka tashi babu komai.

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Atiku Abubakar/Prof Yemi Osinbajo/ Rabiu Kwankwaso
‘Yan siyasan da ba su ji dadin 2023 ba Hoto: Atiku Abubakar/Prof Yemi Osinbajo/ Rabiu Kwankwaso
Asali: Facebook

'Yan siyasan da suka yi rashi a 2023

1. Atiku Abubakar

Atiku Abubakar ya dade yana neman mulkin Najeriya, wasu sun yi tunani zai kai labari a 2023 amma sai ga shi Bola Tinubu ya doke shi a karawar farko.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. Yemi Osinbajo

Kara karanta wannan

‘Yan siyasan PDP da APC da su ka halarci zaman sulhun da Tinubu yayi wa Wike da Fubara

A matsayinsa na mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya fadi babu nauyi da ya nemi tikitin jam’iyyar APC, sai ga shi ya zo na uku a zaben.

3. Rotimi Amaechi

Tsohon gwamnan Ribas ya ajiye Minista domin ya zama ‘dan takaran APC amma bai dace ba kuma shi da magoya bayansa sun ji kunya a zaben Ribas.

4. Abdullahi Adamu

A matsayinsa na shugaban jam’iyya, Abdullahi Adamu yana kallo APC ta rasa kujerar Sanatoci kuma ta ke fama a kotu wajen rike mulkin jihar Nasarawa.

5. Samuel Ortom

A jerin na mu akwai Samuel Ortom wanda ya gagara zama Sanata a Benuwai. APC ta karbe mulki a jihar sannan Ortom bai iya hana a doke Peter Obi ba.

6. Ovie Omo-Agege

Ovie Omo-Agege ya bar matsayin mataimakin shugaban majalisa domin zama gwamna amma bai yi nasara ba kuma bai samu wani mukami ba.

7. Ifeanyi Ugwuanyi

Ifeanyi Ugwuanyi bai tsira da komai a 2023 ba domin Okechukwu Ezea na LP ya doke shi a zaben Sanata, da kyar ya samu PDP ta gaji kujerarsa a Enugu.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu ya tsaida lokacin da mutane za su fara jin dadin Gwamnatinsa

8. Okezie Ikpeazu

Shi ma Okezie Ikpeazu ya ki goyon bayan Atiku Abubakar amma Bola Tinubu bai ba shi mukami ba, kuma APGA da LP sun doke shi a zaben Sanatan Abia.

9. Darius Ishaku

Idan ana so gwamnonin da su ka sha kasa a zaben Sanata, dole a lissafa da Darius Ishaku wanda David Jimkuta ya hana shi zama Sanatan Taraba ta Kudu.

10. Ben Ayade

Ben Ayade bai iya cin zaben majalisar dattawa a APC ba kuma ko da aka je kotu bai yi nasara ba. Da aka tashi nada Ministoci, sai aka dauko kwamishinarsa.

11. Dino Melaye

Sanata Dino Melaye ya yi kokari wajen tallata Atiku Abubakar a zaben bana amma ba a dace ba. Bayan watanni ya nemi zama Gwamnan Kogi, ya zo na uku.

12. Aisha Dahiru Binani

Aisha Dahiru Binani ta fadi zaben gwamnan Adamawa kuma ba ta samu nasara a kotu ba bayan ta bar majalisar dattawa sannan ba ta a Ministocin tarayya.

Kara karanta wannan

Duka yarjejeniya 8 da aka dauka wajen sasanta Wike da Gwamna Fubara a Aso Rock

13. Ibrahim Shekarau

Ibrahim Shekarau ya samu tikitin zama Sanata amma ya fice daga NNPP zuwa PDP. A karshe dai Atiku Abubakar bai iya tabuka komai a jihar Kano ba.

14. Rabiu Musa Kwankwaso

Rabiu Musa Kwankwaso bai je ko ina a zaben shugaban kasa ba, har a wasu jihohin Arewa jam’iyyarsa ta NNPP ta zo bayan LP a zaben shekarar nan.

Ana tunanin Bola Tinubu zai ba shi mukami sai aka ga kotu tana neman tsige NNPP a Kano, amma dai ya tsira da ‘yan majalisun dokoki da tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel