Tinubu Ya Soki Gwamnan PDP a Zaman Sulhu da Mai Gidansa, Ya Kawo Misalin Rikicin Siyasarsa a Legas

Tinubu Ya Soki Gwamnan PDP a Zaman Sulhu da Mai Gidansa, Ya Kawo Misalin Rikicin Siyasarsa a Legas

  • Shugaba Bola Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wurin kawo karshen rikicin siyasar jihar Rivers
  • Tinubu ya yi wata ganawa da Gwamna Fubara da Wike da kuma sauran masu ruwa da tsaki
  • Sai dai shugaban ya soki matakin da gwamnan Rivers ya dauka na rushe ginin Majalisar jihar inda ya ce ya sabawa dimukradiyya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya soki Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers yayin da ya ke sulhunta su da Nyesom Wike.

An yi ganawar ce a Litinin 18 ga watan Disamba a fadar shugaban kasa da ke Abuja, Legit ta tattaro.

Tinubu ya soki gwamnan PDP yayin zaman sulhu da mai gidansa
Tinubu ya bai wa Gwamna Fubara laifi a rikicin Rivers. Hoto: Nyesom Wike, Bola Tinubu, Sim Fubara.
Asali: Facebook

Mene dalilin ganawar da Tinubu?

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu ya bankawa Gwamnan PDP masifa gaban jama’a a fadar Aso Rock Villa

Ganawar ta samu halartar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da mai ba da shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun hada da tsohon gwamnan jihar Rivers, Peter Odili da shugabannin jam'iyyun PDP da APC a jihar.

Wannan na zuwa ne yayin da rikicin siyasar jihar ke kara dagule wa tsakanin Gwamna Fubara da mai gidansa, Nyesom Wike.

Yayin zaman, Tinubu ya caccaki Gwamna Fubara kan rushe ginin Majalisar jihar inda ya ce hakan rage martabar dimukradiyya ce.

Wane martani Tinubu ya yi kan Majalisar jihar?

Tinubu ya tabbatar da himmatuwarshi wurin inganta dimukradiyya inda ya ce ya koka yadda gwamnan ya rushe Majalisar da ake tutiya da ita a dimukradiyya.

Ya ba da misalin lokacin da ya ke gwamnan Legas inda 'yan Majalisa su ka kalubalance shi, ya mutunta su inda ya nemo hanyar gyara matsalar.

Kara karanta wannan

Wike vs Fubara: Shugabannin jam'iyyar PDP na ƙasa sun shiga taron gaggawa a Abuja kan abu 1

Har ila yau, ya ba da misalin lokacin da ya cire Akinwumi Ambode a kan mulki inda ya ce sai da ya bari lokacin zabe, cewar Premium Times.

Rahotanni sun tabbatar cewa wannan sako ne ga Wike don ganin ya kawo karshen rikicin siyasar jihar cikin lalama ba tare da ta da jijiyoyin wuya ba.

An rushe Majalisar jihar Rivers

A wani labarin, Gwamna Siminalayi Fubara ya umarci rushe Majalisar jihar Rivers.

Wannan rushe Majalisar bai rasa nasaba da rikicin siyasar jihar da ke kara ta'azzara tsakanin Gwamna Fubara da Nyesom Wike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel