Gwamna Fubara: Dalilin da Ya Sa Gwamnati Ta Rushe Ginin Majalisar Dokokin Jihar Rivers

Gwamna Fubara: Dalilin da Ya Sa Gwamnati Ta Rushe Ginin Majalisar Dokokin Jihar Rivers

  • Biyo bayan fara rushe ginin majalisar dokokin jihar Rivers, gwamnan jihar Siminalayi Fubara ya bayyana dalilin da ya sa ya dauki wannan mataki
  • A cikin wata sanarwa da kwamishinan watsa labarai na jihar ya fitar a ranar Litinin, Gwamna Fubara ya ce gwamnati za ta sake gina majalisar gaba daya
  • Gyaran majalisar dai ya biyo bayan wani farmaki da aka kai wa majalisar inda wani abin fashewa ya girgiza ginin, yayin da gobara kuma ta tashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Rivers - Gwamnatin jihar Rivers ta ce ta yanke shawarar rushewa tare da gina sabon ginin majalisar dokokin jihar biyo bayan wata gobara da ta lalata wani sashe na majalisar.

Kara karanta wannan

Majalisar Rivers ta kori 'yan majalisu 25 da suka sauya sheka, Fubara ya gabatar da kasafin 2024

Gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ya sanar da hakan a ranar Laraba a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kwamishinan watsa labarai na jihar, Mr. Joseph Johnson.

Siminalayi Fubara/Jihar Rivers
Gwamna Fubara ya ce ya yanke shawarar rushewa tare da gina sabon ginin majalisar jihar biyo bayan gobara da ta lalata wani sashe na majalisar. Hoto: @SimFubaraKSC
Asali: Twitter

Sanarwar ta ce Fubara ya yanke shawarar sake gina majalisar bayan ziyartar inda gobarar ta lalata, kuma kwararru a harkar gine-gine ne suka bayar da shawar yin hakan, rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matakin da gwamnati ta dauka kan ginin majalisar jihar

Kwanishinan watsa labaran ya ce a daren ranar da aka farmaki majalisar, wani abin fashewa da ya tashi ya girgiza kafatanin ginin majalisar, wanda ya zama hatsari ga mutane su shige shi.

Sanarwar ta ce:

"Bayan gudanar da bincike kan karkon ginin, kwararru sun ba gwamnati shawarar gujewa amfani da zauren majalisar, tare da bukatar a sake gina sabuwa."

Johnson ya yi nuni da cewa gwamnati ta yi kokari wajen bin matakan rage kashe kudi don gyara ginin majalisar, tare da daga darajarsa don gogayya da na manyan jihohi.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Rikici ya sake barkewa yayin aka fara rushe Majalisar jihar PDP, an bayyana dalili

Vanguard ta ruwaito sanarwar na cewa Gwamna Fubara ya amincewa 'yan majalisar jihar su yi amfani da wani sashe da ke cikin fadar gwamnatin jihar don gudanar da ayyukansu na wucin gadi.

Gwamna Fubara ya gabatar wa majalisar Rivers kasafin 2024

Gwamna Siminalayi Fubara, ya isa majalsiar jihar Rivers don gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 na jihar, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Gwamnan ya isa matsugunnin majalisar da ke a fadar gwamnatin jihar da misalin karfe 9 na safiya, wanda ya samu tarbar kakakin majalisar, Edison Ehie.

Asali: Legit.ng

Online view pixel