Yadda Tinubu Ya Bankawa Gwamnan PDP Masifa Gaban Jama’a a Fadar Aso Rock Villa

Yadda Tinubu Ya Bankawa Gwamnan PDP Masifa Gaban Jama’a a Fadar Aso Rock Villa

  • Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya kira taro na musamman domin ya yi sulhu tsakanin Siminalayi Fubara da Nyesom Wike
  • Shugaban Najeriyan bai ji dadin yadda aka ruguza ginin majalisar dokoki ba, saboda haka ya yi kaca-kaca da gwamnan Ribas
  • Mai girma Bola Tinubu ya aikawa Nyesom Wike sako da kurman baki domin ganin wutan rikicin siyasar jihar Ribas ta lafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - A ranar Litinin da aka zauna domin a sasanta Siminalayi Fubara da Nyesom Wike, abubuwa da-dama sun faru cikin Aso Villa.

Sai daga baya labari ya fito daga Premium Times cewa Bola Ahmed Tinubu ya yi kaca-kaca da gwamna Siminalayi Fubara a taron.

Kara karanta wannan

Tsohon Ministan Buhari ya ci gyaran Shugaba Tinubu a kan abubuwa 2 da ya aikata a ofis

Tinubu Fubara da Wike
Bola Tinubu zai sasanta Simi Fubara da Nyesom Wike Hoto: Nyesom Wike, Siminalayi Fubara, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Gwamna ya rusa majalisar jihar Ribas

Majiyoyi sun tabbatar da Mai girma shugaban kasa ya soki gwamnan na jihar Ribas ne saboda yadda aka ruguza majalisar dokoki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai ji dadin yadda gwamnatin Simi Fubara ta rusa ginin majalisa saboda sabaninsa da mai gidansa ba.

Bola Ahmed Tinubu ya kira lamarin keta alfarmar tsarin damukaradiyya a Najeriya.

Yadda Gwamna Fubara ya fusata Tinubu

Tinubu ya ce ya shafe rayuwarsa domin tabbatar da mulkin farar hula, bai taba tunanin gwamnan zai rusa alamar damukaradiyya ba.

Rahoton ya ce shugaban Najeriyan ya nuna fushinsa kan yadda aka wargaza gini mai tarihi ba tare da an tsira da komai daga ciki ba.

Labarin Tinubu da yake gwamna a Legas

Wasu da su ka halarci taron sun ce Tinubu ya bada labarin yadda ‘yan majalisar dokoki su ka taso shi a gaba da yake mulki a Legas.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya sun fusata yayin da shugaba Tinubu ya umarci gwamnan PDP ya canza kasafin 2024

Shugaban kasar ya ce a karshe dole ya girmama ‘yan majalisar, aka samu maslaha a lokacin, akasin abin da ya faru yanzu a rikicin Ribas.

Har ila yau, Tinubu ya bada misalin sabanin da ya faru tsakaninsa da wani gwamna a Legas, yace ya kyale shi ne sai da zabe ya gabato.

Rahoton ya ce da alamu shugaban kasar yana jefawa Nyesom Wike sako ne a kan yadda ya fito yana yakar magajinsa daga hawa mulki.

Wadanda su ka halarci taron sulhun sun ce shugaban kasa ya nuna babu dalilin tsige Simi Fubara.

A wata uwa duniyar, ana da labari rigimar Philip Shaibu tayi sanadiyyar daina turo masa kason kudinsa na Mataimakin gwamnan Edo.

A dalilin rikicin Kwamred Shaibu da Gwamna Godwin Obaseki aka fatattake shi daga gidan gwamnati, nan gaba za a aji abin da ya faru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel