Bidiyo: Rikici Ya Sake Barkewa Yayin Aka Fara Rushe Majalisar Jihar PDP, an Bayyana Dalili

Bidiyo: Rikici Ya Sake Barkewa Yayin Aka Fara Rushe Majalisar Jihar PDP, an Bayyana Dalili

  • Da sanyin safiyar yau Laraba ce aka fara rusa Majalisar jihar Rivers tun bayan samun hatsaniya a ranar 30 ga watan Oktoba
  • An gano manyan motocin rusau akalla guda 10 sun fara rusa wani bangare don sauya fasalin Majalisar
  • Wannan na zuwa ne bayan kakakin Majalisar da mambobin da ke goyon bayan Gwamna sun yi zama a Majalisar kafin fara rushe ta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Yayin da rikicin siyasar jihar Rivers ke kara kamari, an fara rusa harabar Majalisar jihar.

Da safiyar yau ce Laraba 13 ga watan Disamba aka gano manyan motocin rusau akalla 10 inda su ka fara rushe Majalisar.

Kara karanta wannan

Yayin da ake rikicin siyasa, kotu ta yi hukunci kan sahihancin kakakin Majalisar PDP, ta yi gargadi

Rikicin siyasar Rivers ya kara tsami yayin da aka fara rushe Majalisar jihar
Manyan motoci sun fara rushe Majalisar jihar Rivers. Hoto: Siminalayi Fubara.
Asali: Facebook

Mene dalilin rushe Majalisar?

Wannan na zuwa ne bayan kakakin Majalisar da mambobin da ke goyon bayan Gwamna Fubara sun yi zama a Majalisar kafin fara rushe ta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin Majalisar ya ce za a gyara Majalisar ce tun bayan da abin fashewa ya ruguza bangaren Majalisar, cewar Punch.

Ehie ya ce Gwamna Fubara ya yi alkawarin samar da wani wuri da ya dace don ci gaba da zaman Majalisar, cewar Daily Trust.

An fara rusa Majalisar ne da sanyin safiyar yau Laraba inda aka jibge jami'an tsaro a harabar Majalisar don gudun abin da ka iya faruwa.

Wane hukunci kotu ta yanke a jiya?

Hakan na zuwa ne kwana daya bayan kotu ta yi hukunci ka rikicin shugabancin Majalisar a jiya Talata 12 ga watan Disamba, cewar Channels TV.

Yayin hukuncin, kotun ta tabbatar na sahihancin shugabancin kakakin Majalisar, Edison Ehie wanda ke tsagin Gwamna Siminalayi Fubara.

Kara karanta wannan

Allah Sarki: Mahara sun sace babban Sarki bayan hallaka hadiminsa da ya yi kokarin hana garkuwar

Kotun ta kuma gargadi wasu daga cikin 'yan Majalisun da su guji shiga zaman Majalisar bayan ta da tarzoma a kwanakin baya.

'Yan Majlisa 27 sun koma APC a Rivers

A wani labarin, akalla 'yan Majalisa 27 ne daga cikin 32 a jihar Rivers su ka sauya sheka zuwa APC daga PDP.

Wannan na zuwa ne bayan rikicin siyasar jihar ya kara tsami tsakanin Gwamna Fubara da Nyesom Wike wanda a yanzu shi ne Ministan Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel