Ban San Yadda Yaro na Ya Samu Takara ba, Sai Dai Na Gani a Facebook Inji Sule Lamido

Ban San Yadda Yaro na Ya Samu Takara ba, Sai Dai Na Gani a Facebook Inji Sule Lamido

  • Sule Lamido ya maidawa masu sukarsa martani saboda PDP ta tsaida yaron shi a matsayin ‘dan takaran Gwamna
  • Tsohon Gwamnan ya nesanta kan shi daga hannu wajen takarar Mustafa Sule Lamido, ya ce a Facebook ya ji labarin
  • Sule ya ce mutane ba su ganin irin wahalar da ya sha a siyasa tun daga zamansa ‘dan majalisa a PRP har zuwa yau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jigawa - A wata doguwar hira da ‘yan jarida suka yi da shi, Sule Lamido ya tattauna kan abubuwan da su ka shafi siyasa da cigaban kasa.

Alhaji Sule Lamido ya yi wa Daily Trust bayanin siyasar Jigawa, inda yaronsa watau Mustafa Sule Lamido ya yi takarar gwamna a PDP.

Sule Lamido
Sule Lamido da yaronsa da ya yi takara a PDP Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Sai dai Sule Lamido ya gani a Facebook

Duk da yana tsohon gwamna kuma jagora a PDP, ‘dan siyasar ya rantse cewa bai san ta yadda Mustafa Sule Lamido ya samu tikitin 2023 ba.

Kara karanta wannan

Jami’an Tsaro sun cika ko ina, NNPP da APC sun hakura da zanga zanga a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Sule Lamido, a Facebook ya samu labarin PDP ta tsaida yaron cikin na sa, kuma babu wanda ya yi masa bayanin yadda aka yi.

"A game da batun yaro na, na rantse da Allah, ban san yadda ya zama ‘dan takara ba.
Jam’iyya (PDP) ba ta taba yi mani bayani ba, na rantse a shafin Facebook na gani.
Yanzu mutane su na cewa na kakaba yaro na a jam’iyyar, shiyasa mu ka sha kashi, haka ne ko. "

- Sule Lamido

Gwagwarmayar Sule Lamido a siyasa

Tsohon Ministan ya ce ya sha wahala a tarihin siyasarsa, har a lokacin da PDP ta na mulki duk su ne suka kafa jam’iyyar a shekarar 1998.

Sule ya zargi Goodluck Jonathan da kai shi kotu, ana masa zargin sata tare da ‘ya ‘yansa saboda maslahar siyasar tsohon shugaban kasar.

Kara karanta wannan

Wike: Yadda Gwamnan Ribas Ya Tura a Kona Majalisar Dokoki Domin Hana a Tsige Shi

"Ana ta suka na. Amma ba a duba gudumuwa ta tun daga 1979 a majalisar wakilan tarayya.
Duk irin abubuwan da na gamu da su na wulakanci, tozarci, da wahala har Jonathan ya gurfanar da ni da ‘ya ‘ya na a kotu."

- Sule Lamido

Sule Lamido ya ce duk abin da za a fada a game da shi ko yaronsa, ba zai damu ba, ya ce zai yi duk bakin kokarinsa wajen bautawa kasar nan.

Siyasar APC da shari'ar zaben Gwamna

Ana da labari Gwamnan jihar Nasarawa ya yi kus-kus da Abdullahi Umar Ganduje awanni bayan APC ta yi galaba kan PDP a shari’ar zabe.

Zuwa yanzu APC ta yi nasara a Kano, Nasarawa, Zamfara da Filato a shario’in zabe, gaba daya jihohin da aka karbe na ‘yan hamayya ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel