'Dan Sule Lamido ya lashe zaben fidda gwanin yan takarar gwamnan Jigawa

'Dan Sule Lamido ya lashe zaben fidda gwanin yan takarar gwamnan Jigawa

  • Kamar mahaifinsa, Mustafa Lamido ya tsallake matakin farko na zama gwamnan jihar Jigawa
  • Dan tsohon gwamnan ya lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar adawa ta jihar, Peoples Democratic Party PDP
  • Mustafa Lamido ya yi kira ga mambobin jam'iyyar su bashi hadin kai don samun nasara a zabe

Dutse - Mustafa Lamido, dan tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya lashe zaben fidda gwanin yan takarar gwamnan a Jigawa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP.

Baturen zaben fidda gwanin, Isah Ahmed, ya bayyana hakan lokacin ya sanar da sakamakon zaben ranar Laraba a Dutse, rahoton Daily Nigerian.

Isah Ahmed ya sanar da cewa Mustafa Lamido ya samu kuri'u 829 cikin mutum 832 da suka ka'da kuri'a yayinda abokin hamayyarsa Saleh Shehu bai samu kuri'a ko guda ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan Borno a 2023: Dan takarar PDP ya zargi Zulum da son kai, ya sha alwashin tsige sa daga mulki

Mustafa ya bayyana farin cikinsa bisa wannan nasara kuma ya yi kira ga yan jam'iyyar su bashi amanar gyara jihar Jigawa idan suka samu nasara.

Yace:

"Ina kira ga ku nisanci siyasar rabuwar kai. Jihar nan ta fi kowannenmu. Yayinda mukzamu shiga mataki na gaba na kamfe da zabe, ina kira ga ku yarda da ni, kuyi aiki dani, kuyi min kamfe kuma ku zabe ni saboda mu gyara jihar."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Babandi Ibrahim, a jawabinsa ya bayyana cewa jam'iyyar zatayi iyakan kokarinta wajen lashe zaben gwamnan jihar.

'Dan Sule Lamido ya lashe zaben fidda gwanin yan takarar gwamnan Jigawa
'Dan Sule Lamido ya lashe zaben fidda gwanin yan takarar gwamnan Jigawa Hoto: Channels TV
Asali: Twitter

Shirin 2023: Tsoffin gwamnonin Jigawa sun gama kai a PDP, domin kassara APC a jihar

A ranar Litinin ne tsohon gwamnan jihar Jigawa, Saminu Turaki, ya koma jam’iyyar PDP inda ya kawo karshen zamansa a jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan.

Kara karanta wannan

Innalillahi: ‘Yan bindiga sun bindige tsohon kwamishina, sun sace ‘ya’yansa mata

Turaki ya koma PDP ne tare da jiga-jigan ‘yan siyasa na jam’iyyar APC na gundumarsa ciki har da tsohuwar kwamishiniyar harkokin mata a jihar, Ladi Dansure.

Tsohon gwamnan ya shaidawa manema labarai a gidansa na Kano cewa ya koma jam’iyyar PDP ne domin ciyar da jihar Jigawa gaba da kuma ‘yantar da jama’a daga mulkin kama-karya na 'yan APC.

A kalamansa:

"A matsayina na shugaba ban koma PDP don samun wani matsayi ba amma, zan yi iya kokarina na jagoranci jam'iyyar zuwa ga nasara a zaben 2023 mai zuwa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel