Sule Lamido: An Kira Ni Fasto A Arewa Saboda Goodluck Jonathan

Sule Lamido: An Kira Ni Fasto A Arewa Saboda Goodluck Jonathan

  • Alhaji Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa ya ce an kira shi fasto tare da daukansa bare a arewa saboda ya goyi bayan Jonathan
  • A wani bidiyo da ke yawa a dandanlin sada zumunta, an jiyo Lamido na cewa Jonathan bai yi wa PDP adalci ba duba da cewa ita ce sanadin duk abin da ya samu a rayuwa
  • Lamidon ya zargi Jonathan da yin watsi da jam'iyyar ta PDP duk da cewa ita ce sanadin duk wani girma da ya ke ganin ya samu a Najeriya da duniya

Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce ya sha suka sosai, har da kiransa fasto a arewa, saboda goyon baya da ya bawa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Daily Trust ta rahoto.

Ya bayyana hakan ne a hirar da aka yi da shi a Arise TV. Babu tabbas ko a yan kwanakin nan aka yi hirar amma bidiyon na yawo a kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan Ya Zama Dan Gudun Hijira, In Ji Gwamnan Bayelsa

Lamido da GEJ
Sule Lamido: An Kira Ni Fasto Saboda Goodluck Jonathan. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tsohon gwamnan wanda mamba ne na jam'iyyar PDP ya zargi Jonathan da yin watsi da PDP, wacce ita ce ta kawo shi matsayin da ya tsinci kansa a yau.

Ya ce:

"Ina matukar tausayin Jonathan. Ina ji masa haushi. Mutum ne wanda shekaru goma da suka wuce ba a san shi ba a Najeriya. Tsohon direkta, sai mataimakin gwamna, sannan gwamna, sai mataimakin shugaban kasa sai shugaban kasar Najeriya.
"Duba tashinsa - duk a PDP ne. PDP ta bashi komai a rayuwa. Ba bashi babban kyauta da kowa a PDP zai iya samu. Su nawa a PDP suka zama shugaban Najeriya? uku kawai: Obasanjo, Yaradua da shi kansa.
"Ya yi wa PDP adalci? jam'iyyar da ta mayar da shi duk wani abin da ya ke tunanin ya zama, fice, ayyukan kasa da kasa, duk PDP ce. Dalilin PDP ne. Ban ji dadi ba."

Kara karanta wannan

2023: Da Ace Ni Ba Dan PDP Bane, Da Zan Taimaki Peter Obi Ya Zama Shugaban Kasa, Gwamnan Arewa

An kira ni fasto saboda Jonathan - Lamido

Lamido ya kara da cewa an kira shi fasto kuma ana yi masa kallon bare a arewa saboda ya goyi bayan Jonathan.

"An kira ni fasto a arewa saboda Jonathan. Na mara masa baya duk rintsi. A arewa, an min kallon bare, wanda baya son cigaban arewa - saboda na yi imani da Najeriya."

Ba zai taba goyon bayan Tinubu ba: Sule Lamido ya bayyana mutum 2 da Buhari yake so ya tsayar a 2023

A wani rahoton, babban jagoran jam’iyyar PDP, Alhaji Sule Lamido, ya ce yana hasashen juyin mulki a zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Lamido ya ce wannan juyin mulki ne zai kai ga samar da tikitin shugaban kasa na shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan da tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel