“Na Yi Nadamar Tallata Buhari”, Rarara Ya Fadi Gaskiyar Abin Da Ya Faru a Gwamnatin APC, Bidiyo

“Na Yi Nadamar Tallata Buhari”, Rarara Ya Fadi Gaskiyar Abin Da Ya Faru a Gwamnatin APC, Bidiyo

  • Mawakin siyasa a Najeriya, Dauda Abdullahi Rarara ya ce ya yi dana sanin tallata Buhari a matsayin shugaban kasa
  • Rarara ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi wanda hadiminsa, Rabi’u Garba Gaya ya yada a kafar sadarwa
  • Mawakin ya ce Buhari sai da ya yi dama-dama da kasar ya kashe ta kafin ya sake ta inda ya ce kowa ya san gaskiya

Jihar Kano – Shahararren mawakin siyasa, Dauda Kahuru Rarara ya caccaki Buhari kan irin yadda ya gudanar da mulki a kasar.

Rarara ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da hadiminsa, Rabi’u Garba Gaya ya yada a kafar sadarwa.

Rarara ya caccaki Buhari kan yadda ya lalata kasar Najeriya
Rarara ya yi martani kan tabarbarewar mulkin Buhari. Hoto: Muhammadu Buhari, Dauda Rarara.
Asali: Facebook

Meye Rarara ke cewa kan Buhari?

Kahutu ya ce Buhari sai da ya kashe kasar nan sannan ya sake ta bayan ya lalata komai a kasar.

Kara karanta wannan

Wani Mutum Ya Yi Ikirarin Soya Kaza Da Ruwa, Ya Saki Bidiyon Tsarin Da Ya bi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ya kamata mutane su fito su fadi gaskiya amma sun gagara inda ya ce a lokacin PDP an bayyana cewa kasar a mace ta ke don haka mutane su ka amince da Buhari.

A cewarsa:

“Sun kasa fitowa su fada wa mutane gaskiya, Buhari sai da ya kashe kasar nan sannan ya sake ta, Buhari ya yi dama-dama da kasar nan, su fito su fadi gaskiya ba wani abu ba ne.
“Lokacin da mu ka karbi mulki a hannun PDP, an fada an ce kasar nan a mace ta ke, abin da ya sa mutane su ka yi wa Buhari uzuri kenan, me yasa mu yanzu za mu boye.”

Shin Rarara ya yi dana sanin tallata Buhari?

Mawakin ya ce ya yi dana sanin tallata Buhari ta wani bangare sannan a wani bangare bai yi ba, saboda kyakkyawan zaton da ya yi wa Buhari.

Kara karanta wannan

“Ina Samu a Wajen Wata Matar”: Magidanci Ya Koka Yayin da Matarsa Ke Hana Shi Hakkinsa Na Aure

Ya ce da ya san abin da ke kasa da bai yi wannan talle na Buhari ba, sai dai ya ce bai yi dana sani ba saboda ya yi ne don Allah.

Ya kara da cewa tabbas ya yi makauniyar soyayya amma mutane sun san gaskiya kuma sun yi shiru bayan ya yi dama-dama da kasar.

Mawaki Rarara ya gamu da iftila’in hatsarin mota

A wani labarin, mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya gamu da tsautsayin hatsarin mota.

Sai dai an tabbatar cewa mawakin bai samu ko kwarzane ba, lamarin ya faru ne yayin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa filin tashi da saukan jiragen sama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel