Dauda Rarara Ya Raba Buhuna 1,040 Na Kayan Abinci a Mahaifarsa Da Ke Jihar Katsina

Dauda Rarara Ya Raba Buhuna 1,040 Na Kayan Abinci a Mahaifarsa Da Ke Jihar Katsina

  • Shahararren mawaƙin siyasa Dauda Kahutu Rarara, ya yi rabon kayayyakin abinci ga mabuƙata a Katsina
  • Rarara ya raba ƙananun buhunan masara 1,040 ga mutane mabuƙata don tallafa musu wajen hidimar iyali
  • Haka nan mawaƙin ya ba da naira 3,000 na cefane, ga kowane daga cikin mutanen da aka bai wa kayan abincin

Katsina - Shahararren mawaƙin nan na siyasa Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara, ya yi rabon buhuna 1,040 na kayan abinci ga mabuƙata.

Babban mai taimakawa mawaƙin a kafafen sada zumunta, Rabi'u Garba Gaya ne ya bayyana hakan a zantawarsa da wakilin Legit.ng.

Rarara ya raba buhunan masara 1,040 a Kahutu
Dauda Kahutu Rarara ya raba buhunan masara 1,040 ga mabuƙata a mahaifarsa. Hoto: Rabi'u Garba Gaya
Asali: Facebook

An bai wa mutane 1,040 buhunan masara ɗaya kowanensu

Rabiu Gaya ya shaidawa Legit.ng cewa, Rarara ya gudanar da wannan rabo na kayan abinci ne a mahaifarsa Kahutu da ke ƙaramar hukumar Danja, jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnan Jihar Arewa Ya Sanya Dokar Kulle a Jiharsa, Ya Bayyana Kwakkwaran Dalili

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An bai wa kowane daga cikin mutane 1,040 ƙaramin buhun masara guda ɗaya domin tallafa masa wajen ciyar da iyalansa.

Mawaƙin ne da kansa ya jagoranci rabon buhunan masaran da ya ce an bayar da su ga mutanen da suka dace.

Rarara ya rabawa mutanen kuɗaɗen cefane

Haka nan Rabi'u Gaya ya kuma shaidawa Legit.ng cewa, Rarara ya gwangwaje kowane daga cikin waɗanda suka samu buhun masarar da naira 3,000 na cefane.

Ya kuma ƙara da cewa, an zaɓo mutanen da ake ganin yafi dacewa a bai wa tallafin ne ba tare da la'akari da bambancin jam'iyya ko ra'ayi ba.

Mafi yawan waɗanda suka amfana da tallafin tsofaffi ne da ƙarfinsu ya ƙare da kuma mata da mazajensu suka rasu.

Rabon kayan abincin da mawaƙi Dauda Kahutu Rarara ya yi, na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan Najeriya ke ci gaba da kokawa dangane da tsadar rayuwa da jefasu cikin yanayi na takura.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Hana Ministan Da Tinubu Ya Zabo Daga Rike Mukami? Lauya Ya Bayyana Gaskiya

Kwamitin rabon kayan tallafin Tinubu ya fitar da sabbin bayanai

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto, kan bayanin da kwamitin rabon kayan tallafi na Shugaba Bola Tinubu ya yi.

Kwamitin, wanda gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris ke jagoranta, ya ce nan 'yan Najeriya za su yi dariya nan ba da jimawa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel