Mawaki Kahutu Rarara Ya Yi Hatsarin Mota A Hanyar Zuwa Filin Tashin Jiragen Sama

Mawaki Kahutu Rarara Ya Yi Hatsarin Mota A Hanyar Zuwa Filin Tashin Jiragen Sama

  • Jimami yayin da shahararren mawaki, Dauda Kahutu Rarara ya yi hatsarin mota a yau Juma'a
  • Hadiminsa a bangaren yada labarai, Rabi'u Garba Gaya shi ya bayyana haka a shafinsa na Facebook
  • Gaya ya ce mawakin bai ji ciwo ba kuma ya na cikin koshin lafiya da taimakon ubangiji

Jihar Kano - Rahoton da muka samu yanzu ya tabbatar cewa shahararren mawaki Dauda Kahutu Rarara ya yi hatsarin mota a dazu.

Hadimin mawakin a bangaren yada labarai, Rabiu Garba Gaya shi ya bayyana a shafinsa na Facebook a yau Juma'a.

Rarara ya yi hatsarin mota a yau Juma'a
Mawaki Kahutu Rarara Ya Yi Hatsarin Mota. Hoto: Rabi'u Garba Gaya.
Asali: Facebook

Meye Gaya ke cewa kan hatsarin na Rarara?

Gaya ya ce Rarara ya yi hatsarin ne a hanyarsa ta zuwa filin tashi da saukan jiragen sama.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP a Arewa Ya Maida Martani Bayan Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Da Ya Samu a 2023

Ya tabbatar cewa mawakin na cikin koshin lafiya inda ya masa addu'ar kariyar Allah a gaba.

Rarara wanda shi ne shugaban kungiyar siyasa ta Kannywood da aka fi sani da 13×13 ya yi hatsarin ne a safiyar yau Juma'a 22 ga watan Satumba.

Yayin sanarwar, Garba Gaya ya yada hotunan hatsarin motar ya nuna yadda ta fada kwalbati inda gaɓar motar ta yi kaca-kaca.

Meye Rarara ya ce kan hatsarin da ya faru?

Sai dai Gaya bai bayyana inda hatsarin motar ya afku ba inda ya ce mawakin na cikin koshin lafiya.

Cikin wata zantawa da mawakin ya yi da DW Hausa, Rarara ya tabbatar da faruwar hadarin.

Sai dai Kahutu Rarara ya ce bai ji ko da kwarzane ba a yayin hatsarin da ta afku a yau Juma'a 22 ga watan Satumba.

Mawakin Rarara ya fara aikin tituna a jihar Katsina

A wani labarin, shahararren mawakin siyasa, Dauda Kahutu Abdullahi wanda aka fi sani da Rarara ya fara aikin gina tituna a wani kauye a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Tare Da Sace Daliban Jami'ar Gwamnatin Tarayya, Bayanai Sun Fito

Hadiminsa a bangaren yada labarai, Rabi'u Garba Gaya shi ya bayyana haka inda ya ce tuni aka fara aikin titunan a yankunan Gaya.

Ya ce Rarara ya fara aikin gina tituna bakwai ne don kauyukan su ci moriyar mawakin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel