Makiyayi Ya Datse Hannun Manomi Saboda Ya Hana Shi Shiga Gona a Kaduna

Makiyayi Ya Datse Hannun Manomi Saboda Ya Hana Shi Shiga Gona a Kaduna

  • An samu fada tsakanin manoma da makiyaya a yankin Damakasuwa dake karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna
  • Fadan har ya kai ga babban ta'adi ga gonar manoman tare da haifar da mummunan rauni ga daya daga cikinsu
  • Dan uwan wanda abin ya shafa ya yi karin haske kan yadda lamarin ya faru tare da bayyana yadda garin ke fama da irin rikicin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Wani makiyayi mai suna Wuzaifa Salisu ya kai hari kan manoma a gonarsu a yankin Damakasuwa dake karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.

Rikicin manoma da makiyaya
Rikici tsakanin manoma da makiyaya ya kai ga yanke hannu a Kaduna. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Manomi ya fara sharar gona a Kaduna

Kara karanta wannan

Yaki da ta'addanci: Ma'aikatar tsaro ta rabawa sojoji sababbin motocin yaki masu sulke

A yayin da makiyayin ya afkawa manomin mai suna Bitrus Chawai ya yanke masa hannu da adda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa tsautsayin ya haɗa da Bitrus Chawai ne a lokacin ya ke sharar gona a shirye-shiryen fara noma na wannar shekarar.

Ɗan uwan manomin mai suna Barnabas ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a jiya Laraba.

Kaduna: Yadda aka sare hannun manomi

Barnabas ya kara da cewa dan uwan nasa ya dawo daga tafiya ne ranar Lahadi domin fara aikin gona sai tsautsayin ya ritsa da shi.

Ya cigaba da cewa a lokacin da Bitrus ta je duba gonarsa sai kawai yaga shanu a ciki suna tafka barna.

Yana fara magana kawai sai makiyayin ya zaro makami ya fara kai masa hari har ya sare masa hannu.

Makiyayin ya yi niyyar kashe Bitrus ne saboda ya kai masa sara ne ta kai amma sai ya kare kayin nasa da hannu, a sanadiyyar haka ne ya sare hannun nasa.

Kara karanta wannan

UNICEF ta ayyana Najeriya a matsayin kasa mafi yawan yara marasa zuwa makaranta

Rikicin manoma da makiyaya a Damakasuwa

A yayin da yake hira da 'yan jarida, Barnabas ya ce ba wannan ne karon farko da makiyaya suka kai hari garin ba.

A cewarsa, a shekarar da ta wuce ma an samu irin haka ta inda makiyaya suka jikkata mutane guda biyu.

'Yan sandan Kaduna ba suyi magana ba

Manema labarai sun yi kokarin jin ta bakin ƴan sandan jihar domin samun karin haske kan lamarin da kuma matakin da za su dauka.

Amma kakakin rundunar ƴan sandan, ASP Mansir Hassan, bai amsa kira da aka masa ta wayar tarho ba.

Manoma da makiyaya sun shiga yarjejeniya

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar manoma da makiyaya sun saka hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya a Kudancin Najeriya.

Dokar wacce ta shafi yankin kudu maso yammacin Najeriya an tabbatar da ita ne a Ibadan hedikwatar jihar Oyo domin kawar da rikicin manoma da makiyaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel