Ba laifinmu ba ne: Sanata Kawu Sumaila Ya Fadi Wadanda Su Ka Hana El-Rufai Minista

Ba laifinmu ba ne: Sanata Kawu Sumaila Ya Fadi Wadanda Su Ka Hana El-Rufai Minista

  • Abdulrahman Suleiman Kawu Sumaila ya ce ba majalisa ta hana Nasir El-Rufai zama Minista ba
  • Sanatan Kudancin Kano ya tabbatar da cewa takarda aka samu daga jami’an tsaro a game da lamarin
  • Kawu Sumaila na alfahari da ayyukan da majalisa ta soma a karkashin jagorancin Godswill Akpabio

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - A wata doguwar zantwaa da aka yi da Abdulrahman Suleiman Kawu Sumaila, ya yi maganar batutuwan da su ka shafi mulki.

A hirar da ya yi da Aminiya, Sanata Abdulrahman Suleiman Kawu Sumaila ya amsa tambayoyi game da irin aikin da su ke yi a majalisar kasa.

A nan aka bijirowa Sanatan mai wakiltar Kano ta kudu tambaya game da albashin ‘yan majalisa, nadin ministoci, rikicin Nijar da sauransu.

El-Rufai
Malam Nasir El-Rufai wajen tantance Ministoci a Majalisa Hoto: www.thecable.ng
Asali: UGC

Tantance El-Rufai a Ministocin Tarayya

Kara karanta wannan

Wahalar da Ake Sha Tamkar Nakuda ce, Bola Tinubu Ya Ce Za a Haifi Jariri

Da yake magana a kan kin yin na’am da Malam Nasir El-Rufai ya zama minista a gwamnatin tarayya, sai ya wanke Sanatoci daga zargi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanata Kawu Sumaila ya ce jami’an tsaro ne su ka nuna akwai ta-cewa a kan tsohon Gwamnan na jihar Kaduna, don haka aka ki tantance shi.

Kafin a gama tambayar, tsohon mai ba shugaban Najeriyan shawara ya yi wuf ya jefa zargin kan wuyan jami’a tsaro, ba tare da karin bayani ba.

Menena ainihin dalilin da ya sa ba ku yarje…?

"Ba mu ne ba mu yarje ba, kawai hukumar tsaro ne su ka aiko mana da takarda cewa akwai wasu abubuwa da ba su gama gamsuwa da su ba, saboda haka mu dakatar da tantance su."

- Suleiman Kawu Sumaila,

Majalisa ta hana yakin Nijar da Najeriya

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Raddi Kan Zargin Zaluntar ‘Yan Arewa a Rabon Mukaman Minista

Daga cikin kokarin da ya ce majalisar tarayya ta goma tayi daga Yuni zuwa yanzu, akwai hana Najeriya shiga yaki da makwabtanta Nijar.

Kamar yadda suka yi tsammani, Sanata Sumaila yake cewa matsayar da su ka dauka a majalisa bai yi wa shugaban kasa Bola Tinubu dadi ba.

Dama can an cire tallafin man fetur

A batun tallafin man fetur kuwa, Sanatan na NNPP ya ce Mai girma shugaban kasa Bola Tinubu ratayar zomo ya yi, amma ba shi ya kashe ba.

Tun a lokacin da Muhammadu Buhari zai bar mulki, bai ware kudin tallafin man fetur ba, ya ce da Tinubu ya zo sai ya sanar da janye tsarin.

A tattaunawar aka ji ya na maida martani ga masu sukar albashinda su ke karba.

Minista: Wike zai iya barin jam'iyyar PDP?

A bangaren siyasa, mun ji labari akwai yiwuwar Nyesom Wike ya koma Jam'iyyar APC bayan ba shi Minista ko dai a kore shi daga jam’iyyar PDP.

Makomar sauran 'Yan G5 kamar Samuel Ortom, Ifeanyi Ugwanyi, Okezie Ikpeazu babu tabbas a PDP da su ka yi fito na fito da jam'iyyarsu a zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel