Sabon Rahoto Ya Bayyana Matsayin Da Ake Sa Ran Tinubu Zai Ba Kwankwaso A Majalisar Ministocinsa

Sabon Rahoto Ya Bayyana Matsayin Da Ake Sa Ran Tinubu Zai Ba Kwankwaso A Majalisar Ministocinsa

  • Akwai yiwuwar ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen da ya gabata, Rabiu Musa Kwankwaso, ya zama ministan tsaron Najeriya, kamar yadda wani rahoto ya nuna
  • Daga shekarar 2003 zuwa 2007, Kwankwaso ya riƙe muƙamin ministan tsaro na ƙasa, wanda Shugaba Obasanjo ya naɗa shi inda ya maye gurbin Theophilus Danjuma
  • Baya ga kasancewarsa tsohon ministan tsaro, Kwankwaso tsohon sanata ne kuma ya yi gwamnan jihar Kano har sau biyu

Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja - Rabi'u Musa Kwankwaso, ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar NNPP, a zaɓen 2023, mai yiyuwa ne ya zama sabon ministan tsaron Najeriya.

A cewar rahoton da jaridar Vanguard ta wallafa a ranar Litinin, 19 ga watan Yuni, mai yiwuwa Kwankwaso ya zama ministan tsaro a gwamnatin Tinubu.

Kara karanta wannan

Shin Dagaske EFCC Ta Gayyaci Tsohon Shugaban Kasa Kan Wawure Kuɗi? Gaskiya Ta Bayyana

Hankalin Tinubu yafi karkata ga Kwankwaso
Akwai yiwuwar Tinubu ya bai wa Kwankwaso ministan tsaro. Hoto: Gov. Abdullahi A. Sule Mandate
Asali: Facebook

Tinubu ya fi mayar da hankali kan Kwankwaso

Wata majiya ta bayyana cewa, duk da cewa akwai waɗanda ke son Shugaba Bola Tinubu ya sanya sunan tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umaru Ganduje, a majalisar ministocin nasa, majiyar ta ce, hankalin Tinubu ya fi karkata ga Kwankwaso.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A dalilin hakan ne, ake sa ran babban jigon NNPP zai shiga cikin jerin sunayen ministocin Tinubu, wanda da alama za a bayyana a wata mai zuwa.

Majiyar ta ce:

‘’Rikicin cikin jam’iyyar APC ya yi ƙamari. Wasu na tura sunan tsohon gwamnan Kano, Umar Ganduje amma Tinubu ya fi karkata ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso.”
“Abin takaici, Ganduje ya rasa jihar Kano kuma a yanzu ba shi da wani tasiri. Akwai yiwuwar Kwankwaso ya zama ministan tsaro.”

Kwankwaso ya bayyana abinda ya tattauna da Shugaba Tinubu

Kara karanta wannan

Gwamna Radɗa Ya Jagoranci Gwamnoni 6 Sun Gana da Tinubu Kan Muhimman Abu 2 da Suka Shafi 'Yan Arewa

A baya dai Legit.ng ta kawo muku rahoto cewa Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano kuma tsohon ministan tsaro, ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya gayyace shi kan rusau da ake gudanarwa a jihar Kano da ya janyo cece-kuce.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, Kwankwaso ya bayyana cewa sai da Ganduje ya kore shi daga jihar Kano a lokacin da yake kan karagar mulki.

Abba Gida Gida zai yi wa matar Ganduje tonon silili

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoton cewa Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya koka kan yadda ya gano cewa mai ɗakin tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ce ta mallaki kaso 70 cikin 100 na filayen makarantun da aka saida.

Abba Gida Gida ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi dangane da rushe-rushen da gwamnatinsa take yi a sassa daban-daban na birnin Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel