Abba Gida Gida: Sabon Gwamna Ya Sake Fito da Tsarin Zuwa Jami’o’in Kasashen Waje

Abba Gida Gida: Sabon Gwamna Ya Sake Fito da Tsarin Zuwa Jami’o’in Kasashen Waje

  • Abba Kabir Yusuf ya bada umarnin a fara shirin tura yaran Kano zuwa jami’o’in kasashen Duniya
  • Sanusi Dawakin Tofa ya fitar da sanarwa cewa an bude shafin yanar gizo domin zakulo dalibai
  • Dole wadanda za a dauko ya zama asalin ‘Dan jihar Kano kuma ya samu shaidar First Class a Digiri

Kano - Wata sanarwa ta fito cewa gwamnatin jihar Kano ta maido tsarin nan na aika yara zuwa jami’o’in kasashen ketare domin su karo ilmin zamani.

Kamar yadda babban sakataren yada labarai na gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya sanar, za a cigaba da kai yara ketare domin digirgir.

Sanarwar ta ce wannan yana cikin yunkurin cika alkawuran da Abba Kabir Yusuf ya dauka a lokacin da yake yakin neman zaben zama Gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da Suka Hana Abdulaziz Yari Zama Sabon Shugaban Majalisar Dattawa

Gwamnan Kano, Abba Gida Gida
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: EngrAbbaKYusif
Asali: Facebook

A halin yanzu Sakataren gwamnatin Kano ya samu umarnin Mai girma Gwamna na daukar wadanda su ka kammala digiri na daya da matakin farko.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tsarin Kwankwasiyya ya dawo

Idan za a tuna, a baya Rabiu Kwankwaso ya fito da wannan tsari a lokacin ya na mulki.

A 2015 gwamnati ta dauki jerin yara 503 na karshe, aka tura zuwa kasashe 14 da ke fadin Duniya domin samun digiri a fannonin ilmi dabam-dabam.

Saboda haka gwamnatin Abba Yusuf ta sanar da duk ‘dan asalin jihar Kano da yake da shaidar digirin farko (First Class) ya yi amfani da wannan dama.

Yadda za a nemi gurbin karatu

Daga cikin sharudan da aka bada shi ne wajibi ne wanda zai amfana da tsarin ya zama mai koshin lafiyan da zai iya tafiya zuwa kasar da aka zaba masa.

Kara karanta wannan

Akwai Dalili: Abba Gida Gida Ya Fadi Hikimar Ruguza Shatale-Talen Gidan Gwamnati

Masu neman gurbin karatu na zangon 2023/2024, za su ziyarci shafin www.kanostategov.ng./scholarship.

Bayan an nemi wannan dama sai a saurari gayyatar tantancewa daga ofishin sakataren gwamnatin Kano, za a dauki kwanaki 14 kafin a rufe shafin.

Sanarwar ta bayyana cewa za a a bukaci takardun haihuwa, shaidar zama ‘dan jiha, takardun makarantun firamare, sakandare da shaidar yin digiri.

An fitar da nadin mukamai

Sanusi Dawakin Tofa ya fitar da sanarwa cewa Gwamnan Kano ya nada Shugabannin KIRS da SEMA da kuma mutum 14 masu bada shawara.

Sanarwar da aka fitar ta ce Abba Kabir Yusuf ya maido Sani Abdulkadir Dambo daga Hukumar FIRS, sannan Alhaji Isiyaku Kubaranci zai jagoranci SEMA.

Asali: Legit.ng

Online view pixel