Majalisar Tarayya Ta Nemi Cin Hancin $150m Daga Binance? Gaskiya Ta Fito

Majalisar Tarayya Ta Nemi Cin Hancin $150m Daga Binance? Gaskiya Ta Fito

  • Yayin da ke ci gaba da shari'a da kamfanin Binance, an bankado wata badakala ta cin hanci da ake zargin Majalisa
  • Binance na zargin wasu daga Majalisar Wakilai da neman karbar cin hanci domin kawar masa da matsala a Najeriya
  • Sai dai Majalisar ta yi fatali da wannan zance inda ta ce babu kamshin gaskiya tattare da labarin neman bata mata suna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Majalisar Wakilai ta yi martani kan zargin karbar cin hanci daga kamfanin Binance da ake yadawa.

Majalisar ta ƙaryata rade-radin inda ta ce babu kamshin gaskiya kan karbar cin hanci daga kamfanin.

Majalisa ta yi martani kan zargin neman cin hanci daga Binance
Majalisar Tarayya ta ƙaryata neman cin hancin $150m daga kamfanin Binance. Hoto: House of Representatives.
Asali: Facebook

Zargin da Binance ke yi kan Majalisar

Kara karanta wannan

"Yadda aka nemi cin hanci a hannun jami'an Binance a Najeriya"

A jiya Talata 7 ga watan Mayu kamfanin ya ce wasu mutane a Najeriya sun bukaci ya biya makudan kudi domin kawo karshen tuhumarsu da ake yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanin Binance ya zargi wasu manyan jami'an gwamnatin Najeriya da neman cin hancin $150m a kuɗin kirifto domin a kawo ƙarshen tuhumar da ake masa.

Shugaban kamfanin, Richard Teng ne ya bayyana haka inda ya ce Tigran Gambaryan, jami'i a kamfanin ya yi iƙirarin cewa ya samu wani saƙo mai ɗaga hankali inda aka ba kamfanin kwana huɗu ya biya $150m a kuɗin kirifto.

Wane martani Majalisar ta yi kan Binance?

Shugaban Majalisar, Tajudden Abbas ya koka kan yadda aka hada wannan labari domin cimma wani buri, cewar TheCable.

Abbas ya ce babu inda wani kwamitin Majalisar ya gana da wanda ya yi zargin karbar cin hanci, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

Majalisa ta gayyaci kamfanonin siminti domin amsa tambayoyi kan tashin farashi

"Zamu yi amfani da duk wata kafar sadarwa domin ƙaryata wannan zargi da ake yi."
"Babu wani abu makamancin haka da ya faru, babu kwamitin wannan Majalisar da ya hadu da wannan mutumin."

- Tajudden Abbas

Yayin zaman majalisar a jiya Talata 7 ga watan Mayu, mamban Majalisar daga jihar Ebonyi, Kama Nkemkanma ya ƙaryata labarin da ake yadawa.

Kama ya ce babu wanda Majalisar ta nemi zama da shi har ta bukaci cin hanci daga gare su kan matsalar da suke ciki.

"Wannan Majalisar ta fi karfin a durkusar da ita tare da bata mata suna."
"Wannan zargi zai bata sunan Majalisar kuma bai kamata a yi wasa da hakan ba."

- Kama Nkemkanma

Tinubu zai dakile masu kasuwancin Kirifto

A wani labarin, Gwamnatin Tarayya ta sake juyowa kan masu kasuwancin Kirifto ba bisa ka'ida ba da ke kawo cikas ga tattalin arziki.

Hukumar SEC ita ta bayyana haka inda ta ce za ta tsaurara matakai domin inganta darajar Naira a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel