Shugaba Tinubu Ya Bayyana Jerin Muhimman Abubuwa 8 Da Gwamnatinsa Za Ta Mayar Da Hankali A Kai

Shugaba Tinubu Ya Bayyana Jerin Muhimman Abubuwa 8 Da Gwamnatinsa Za Ta Mayar Da Hankali A Kai

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya zayyano muhimman abubuwa guda takwas da gwamnatinsa za ta fi mayar da hankalinta a kai
  • Shugaban ya bayyana muhimman abubuwa guda takwas da suka sa a gaban ne yayin da yake jawabi a wajen kaddamar da Majalisar Tattalin Arzikin Kasa (NEC)
  • Shugaban na Najeriya ya ambaci tsaro, tattalin arziki, samar da ayyukan yi, noma, da sauran su, inda ya bukaci gwamnonin jihohi 36 da su mara masa baya

Abuja - A ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana muhimman abubuwa guda takwas da gwamnatinsa za ta bai wa fifiko a lokacin ƙaddamar da Majalisar Tattalin Arziƙin ƙasa (NEC) a fadar gwamnati da ke Abuja.

A wajen taron, Shugaba Tinubu ya kuma ƙaddamar da wata kungiya ta masu ba shi shawara wacce ta ƙunshi gwamnonin jihohi 36, gwamnan CBN, da kuma wasu sauran masu ruwa da tsaki.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Sanya Labule Da Abdulsalam Abubakar a Villa, Bayanai Sun Fito

A rahoton Arise News, Shugaba Tinubu ya buƙaci gwamnonin jihohi 36 da su haɗa kai da shi wajen ganin an ceto tattalin arziƙin Najeriya daga halin da yake ciki na tsawon shekaru na tsawon shekaru masu yawa.

Tinubu ya bayyana muhimman abubuwan da ya sa gba
Tinubu ya bayyAsana muhimman abubuwa guda 8 da gwamnatinsa ta sa gaba. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tinubu ya ce gwamnatinsa ta fara ɗaukar matakai kan tattalin arziƙin ƙasa

Tinubun ya yi kira da a samu haɗin kai tsakaninsa da gwamnoni da sauran muƙarrabansa domin biyawa 'yan Najeriya buƙatunsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban kasar ya bayyana cewa tuni aka fara tsarin gyara tattalin arzikin ƙasar, inda aka fara da cire tallafin man fetur da kuma daidaita kan farashin kasuwar canjin kuɗaɗe.

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali ne kan tsaro, tattalin arziƙi, ayyukan yi, noma, ababen more rayuwa, manufofin kudi, da tallafin mai.

Abubuwa 8 da gwamnatin Tinubu ta sa a gaba

Kara karanta wannan

Abubuwa 4 Da Ake Ganin Suna Da Alaka Da Dakatar Da Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa Da Tinubu Ya Yi

Da yake ƙarin haske, shugaba Tinubu ya zayyano abubuwa takwas da gwamnatin sa ta sa a gaba, inda ya ce:

“Na kuma tattaro ƙa’idojin da za su jagoranci gudanar da gwamnatinmu kamar haka:
1. Rashin nuna bambanci wajen gudanar da mulki bisa kundin tsarin mulki da tabbatar da bin doka da oda.
2. Kare al’umma daga ta’addanci da duk wani nau’i na laifuka.
3. Inganta ci gaban tattalin arziƙi da bunƙasa ƙasa ta hanyar samar da ayyukan yi.
4. Samar da isasshen abinci da kawo ƙarshen talauci.
5. Shigar da mata da matasa a duk ayyukan da za mu riƙa yi.
6. Ɗaukar ƙwararan matakai masu fa'ida kamar haɓaka al'adun bayar da bashi.
7. Daƙile cin hanci da rashawa.
8. Tabbatar da nagartar hukumomin yaki da cin hanci da rashawa."

Tinubu ya naɗa Ribadu, Edun, Darazo, da wasu mutane 5 matsayin mataimakansa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana tsohon shugaban Hukumar Yaƙi Da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati (EFCC), Nuhu Ribadu, a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin tsaro.

Kara karanta wannan

Mohammed Umar Abba: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Shugaban Riko Na EFCC Bayan Magu

Naɗin na Ribadu na cikin naɗe-naɗe guda takwas da shugaban ya yi kamar yadda ya bayyana a wata sanarwa da Abiodun Oladunjoye, daraktan yaɗa labarai na fadar Gwamnatin Tarayya ya fitar a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni.

EFCC ta ƙaddamar da bincike tsoffin ministocin Buhari guda 8

Legit.ng ta kuma kawo muku wani rahoto a baya kan ministocin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari guda takwas da EFCC ta ƙaddamar da bincike a kansu.

EFCC dai na zargin waɗannan ministoci ne da ayyuka na cin hanci da rashawa a lokacin da suke riƙe da mukaman gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel