Kamfanin NNPC Ya Dauki Mataki Domin Kawo Karshen Wahalar Man Fetur

Kamfanin NNPC Ya Dauki Mataki Domin Kawo Karshen Wahalar Man Fetur

  • Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPLC) ya dauki sabon mataki domin kawo karshen dogayen layuka a gidajen mai
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa jami'in yada labaran kamfanin ne, Olufemi Soneye ya bayyana haka ga 'yan Najeriya
  • NNPCL kuma bayyana yadda za su yi haɗaka da jami'an tsaro da masu ruwa da tsaki wurin maganin masu boye mai

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ya ce ya hada kai da jami'an tsaro da masu ruwa da tsaki domin maganin masu boye mai.

NNPC NG
Kamfanin NNPC ya tanadi mai domin saukakawa 'yan Najeriya. Hoto: Benson Ibeabuchi
Asali: Getty Images

Kamfanin ya kara da cewa a yanzu haka ya tanadi man fetur da zai wadatar da 'yan kasa har na sama da wata guda.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta dawo da lantarki a garuruwan da aka yi shekaru babu wuta a Sokoto

NNPC ya yi wa 'yan Najeriya tanadi

Jaridar Leadership ta ruwaito jami'in yada labaran kamfanin, Olufemi Soneye, yana cewa 'yan Najeriya kada su tada hankali domin matsalar man fetur ta zo karshe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Soneye ya ce a halin yanzu layuka sun fara raguwa a wasu gidajen mai kuma da sannu duk za su ragu a fadin Najeriya.

A halin yanzu kamfanin yana da mai da bai gaza lita biliyan 1.5 ba wanda zai wadatar da 'yan Najeriya sama da kwana 30 masu zuwa, cewar Nairametrics

Man fetur ya kara kudi

A wani rahoton kun ji cewa bayanan da hukumar kididdiga ta kasa ta fitar sun nuna cewa ‘yan Najeriya sun shiga tsadar man fetur a watan Fabrairun 2024.

Bayanai sun nuna cewa, farashin litar man fetur ya karu da 157.57% tun watan Faburairun 2024 idan aka kwatanta da watan na Faburairu a 2023.

Kara karanta wannan

Badakalar N80bn: Abin da wasu tsofaffin gwamnoni ke cewa game da Yahaya Bello

Fetur: Jigawa ta saka dokar ko-ta-kwana

A wani rahoton kuma, kun ji cewa biyo bayan dogayen layuka da suka bayyana a gidajen mai, kwamitin ko-ta-kwana ya fara zaga gidajen mai a fadin jihar Jigawa.

Gwamnatin jihar ta ce ta kafa kwamitin ne domin bincike da ladabtar da gidajen da suke boye mai ko kara masa kudi a fadin jihar ba tare da bin ka'ida ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel