"Hakkin Yin Mulki": El-Rufai Ya Fadi Dalilinsa Na Goyon Bayan Tinubu, Musulmi Daga Kudu Don Zama Shugaban Kasa

"Hakkin Yin Mulki": El-Rufai Ya Fadi Dalilinsa Na Goyon Bayan Tinubu, Musulmi Daga Kudu Don Zama Shugaban Kasa

  • Mallam Nasir El-Rufai ya bayyana dalilin da ya sa ya goyi bayan Asiwaju Bola Tinubu, Musulmin Kudu maso Yamma ya zama shugaban ƙasa.
  • El-Rufai ya ce goyon bayansa ga Tinubu ya yi sa ne domin Musulmin yankin Kudu su shigo a dama da su a harkokin mulki
  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna ya bayyana cewa babban daraktan Kungiyar Kare Hakkin Musulmi (MURIC), Farfesa Ishaq Akintola ne ya nemi ya goyi bayan takarar ta Tinubu

Kaduna, jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai , ya bayyana dalilin da ya sa shi da tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle suka goyi bayan musulmin Kudu maso Yamma ya zama shugaban ƙasa a zaben 25 ga Fabrairu da ya gabata.

El-Rufai ya ce ya goyi bayan shugaban ƙasa Bola Tinubu ne domin ya bai wa Musulmin yankin Kudu maso Yammacin ƙasar nan damar shigowa a dama dasu kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

El-Rufai ya bayyana dalilinsa na goyon bayan Tinubu
El-Rufai ya ce saboda a dama da Musulman Kudu a siyasa ya goyi bayan Tinubu. Hoto: Nasir El-Rufai, Asiwaju Bola Ahmed Tinnubu.
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne a Kaduna, yayin da yake zantawa da wasu Malaman addinin Musulunci kan dalilin da ya sa ya yi gwamnatin Musulmi zalla a jihar Kaduna .

Tsohon gwamnan wanda ya yi magana da harshen Hausa, ya bayyana cewa babban daraktan Kungiyar Kare Hakkin Musulmi (MURIC), Farfesa Ishaq Akintola tare da wasu shugabanni daga Legas ne suka kawo masa ziyara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce a ziyarar sun roƙe shi a kan ya goyi bayan Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC a zaɓen 2023.

El-Rufai ya ce:

“Farfesa Akintola ne ya zo shi da shugabanninsu daga Legas inda suka yaba mana kan shawarar da muka yanke na cewa ɗan Kudu ya fito takara."
"Sun ce mana Yarbawan yankin Kudu maso Yamma na da matsala. Musulminsu in ya fito zai nemi shugabanci sai a ce ba dama ya nema domin ba zai ci zaɓe ba. Ba zai ci zaɓe ba don dole sai Kirista daga Kudu maso Yamma ne zai iya fitowa ya nemi shugancin Najeriya sai ya ɗauki Musulmi daga Arewa a ya zama mataimakinsa.”

“Suka ce tun lokacin Abiola ba a sake yi ba, suna son haka. Na ce to ku je ku kawo mana wanda zamu bi. Ya ce Asiwaju, na ce ba ma shiri da shi, (Akintola) ya ce ku shirya don addinin Musulunci, na ce za mu shirya.”

El-Rufai ya ƙara da cewa bayan samun tikitin Tinubu, sai ya duba ya ga ya zama dole ya ɗauki Musulmi matsayin mataimaki, in ba haka ba, ba zai ci zaɓe ba.

Dalilin da ya sa muka goyi bayan Musulmin Kudu maso Yamma

El-Rufai ya ƙara da cewa matakin da ya ɗauka shi da tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle shi ne na goyon bayan Musulmin Kudu maso Yamma don ya mulki Najeriya.

El-Rufai ya ce:

“Na san ni, da gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ba don muna son wani abu muka yi ba. Ƙila sauran suna son wani abu, amma wallahi ni da Bello Matawalle mun ce a yi haka don ai maganin wannan matsalar ta addini, sannan Musulmin Kudu maso Yamma, suma mu basu damar zuwa a dama da su, su yi shugabancin nan.”

“To Allah, duk da taron dangin da aka yi, duk da addini da aka yi amfani da shi, Allah ya ba Asiwaju nasara.”

Zaku iya kallon bidiyon a shafin Fesbuk na The Punch.

El-Rufai ya bayyana abin da ya tayar masa da hankali lokacin zaɓe

A wani labarin da Legit.ng ta kawo muku a baya, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai ya bayyana babban abin da ya tayar masa da hankali lokacin babban zaɓen 2023 da ya gabata.

El-Rufai ya bayyana cewa yadda ya ga ana ta amfani da maƙudan kuɗaɗe wajen siyan kuri'a ne ya tayar masa da hankali lokacin zaɓen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel