Zaben 2023: Gwamna El-Rufai Ya Bayyana Abinda Ya Tayar Masa Da Hankali Lokacin Zabe

Zaben 2023: Gwamna El-Rufai Ya Bayyana Abinda Ya Tayar Masa Da Hankali Lokacin Zabe

  • Gwamnan Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya caccaki mutanen da ke shiga siyasa domin su tara dukiya mai tarin yawa
  • Gwamnan ya bayyana cewa siyasa ta masu ƙan-ƙan da kai ce, ba masu yi mata kallon hanyar samun dukiya ba
  • El-Rufai ya bayyana cewa siyan ƙuri'un da aka yi a lokacin babban zaɓen 2023 ya firgita shi, inda ya yi nuni da cewa ƴan siyasar da suka cancanta sun sha kashi saboda hakan

FCT, Abuja - Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa yadda aka yi amfani da kuɗi wajen siyan ƙuri'u a babban zaɓen 2023, ya tayar masa da hankali.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Lahadi, 21 ga watan Mayun 2023, yayin zantawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Ba Sassauci: Yana Dab Da Sauka Mulki, Gwamna El-Rufai Ya Sha Wani Muhimmin Alwashi

El-Rufai ya firgita kan yadda aka siya kuri'a a zaben 2023
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai Hoto: Premiumtimes.com
Asali: UGC

Kamar yadda PM News ta rahoto, gwamnan ya ce masu kaɗa ƙuri'a sun ƙi yin zaɓe har sai an ba su kuɗi.

"Na ga mutanen kirki da suka yi takara amma sun faɗi zaɓe. Sun sha kashi ne kawai saboda ana ba mai yin zaɓe N5,000 a ranar zaɓe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ka yi tunani kaga dun wanda ya baka kuɗi ka zaɓe shi a lokacin zaɓe. Ka bashi makullan asusun dukiyar al'umma ne har na tsawon shekara huɗu ya je ya mayar da N5,000 ɗinsa."

El-Rufai ya koka kan yadda kuɗi suka yi tasiri a zaɓen 2023

Tsohon ministan na birnin tarayya Abuja, ya bayyana cewa yawan siyan ƙuri'ar da aka yi ya janyo ƴan takarar da suka cancanta, ta kife da su.

Ya yi nuni da cewa irin hakan ne ke sanyawa, ƴan siyasa su sace dukiyar al'umma, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Gwamna Wike Ya Ba 'Yan Takarar Shugabancin Majalisa Muhimmiyar Shawara

El-Rufai ya bayar da shawarar cewa shiga cikin siyasa hidimtawa al'umma ne ba wai hanyar tara dukiya ba, kamar yadda wasu mutane da dama suka ɗauka.

"Idan kana buƙatar kuɗin siyan sutura, ka kiyayi siyasa, siyasa ta masu haƙuri da kaɗan ce, siyasa ta masu son yi wa al'umma aiki ne. Ina fatan mutane za su fahimci hakan saboda abinda na gani ya bani tsoro." A cewarsa.
"Siyasa magana ce kawai ta yi wa al'umma aiki, don haka idan kana neman azurta kan ka, siyasa ba ta ka ba ce.

El-Rufai Ya Kalubalanci Tsofaffin Gwamnonin Kaduna

A wani labarin na daban kuma, gwamna El-Rufai na jihar Kaduna, ya ƙalubalanci tsaffin gwamnonin da suka taɓa mulkin jihar.

Gwamnan ya ƙalubalanci tsaffin gwamnonin da su fito su yi rantsuwa kan cewa ba su taɓa, yi wa dukiyar al'ummar jihar wawura ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel