Uzodinma Ya Aje Mataimakinsa, Ya Ɗauko Mace a Matsayin Mataimakiyar Gwamna

Uzodinma Ya Aje Mataimakinsa, Ya Ɗauko Mace a Matsayin Mataimakiyar Gwamna

  • Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya canja abokin takara yayin da ake tunkarar zaben gwamna a watan Nuwamba
  • Uzodinma ya jingine mataimakinsa, Farfesa Placid Njoku, ya zaɓi mace a matsayin 'yar takarar mataimakin gwamna a APC
  • Masu sharhi kan harkokin siyasa sun bayyana cewa wannan wata dabara ce da APC ta bullo da ita domin cin zaɓe

Imo - Gwamnan jihar Imo kuma sabon shugaban gwamnonin APC, Hope Uzodimma, ya jingine mataimakinsa, Farfesa Placid Njoku, gabannin zaben gwamna jihar mai zuwa.

Daily Trust ta rahoto cewa a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023 za'a gudanar da zaɓen gwamna a jihar Imo da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.

Hope Uzodinma.
Uzodinma Ya Aje Mataimakinsa, Ya Ɗauko Mace a Matsayin Mataimakiyar Gwamna Hoto: dailytrust
Asali: UGC

A jerin sunayen ƴan takara da hukumar zaɓe INEC mai zaman kanta ta saki, ya nuna gwamna Uzodimma ya aje mataimakinsa, ya ɗauko mace, Misis Ekemaru Chinyere Ihuoma, a matsayin 'yar takarar mataimakin gwamna.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani Ya Tona Asirin Wasu Gwamnoni da Suka Rika Ma'amala da Yan Ta'adda a Jihohinsu

Jerin yan takarar ya kunshi ɗan takara a inuwar Peoples Democratic Party (PDP), Samuel Anyanwu, wanda ya zaɓi tsohon ɗan majalisar tarayya, Jones Onyeriri, a mataimakinsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka nan Labour Party ta tura sunan Sanata Athan Achonua matsayin wanda ta tsayar takarar gwamna da kuma tsohon ɗan majalisar tarayya, Tony Nwulu, a matsayin mataimakinsa.

Meyasa gwamnan ya zaɓi mace a matsayin mataimakiya?

Masu sharhi kan siyasa sun bayyana cewa APC ta zaɓi mace a matsayin mataimakiyar gwamna da nufin tattara kuri'un mata waɗanda adadinsu ya fi yawa a Imo.

A hasahensu, APC ta zaɓi Misis Ekemaru, wacce ta fito daga yanki ɗaya da ɗan takarar jam'iyyar PDP domin daƙile tasowa da karɓuwan babbar jam'iyyar Adawa a zaben watan Nuwamba.

Haka nan sabuwar 'yar takarar mataimakin gwamnan tamkar diyya ce ga mazauna yankin Ikeduru saboda ta fito daga tsagin siyasa ɗaya da Placid Njoku, rahoton Leadership ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Wasu Manyan Jiga-Jigan PDP da Ɗumbin Mambobi Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC a Arewa

PDP ta ƙara shiga matsala a jihar Kogi

A wani rahoton kuma Magoya bayan PDP sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a jihar Kogi Yayin da zaben gwamna Ke kara matsowa.

Jiga-jigai kuma tsofaffin shugabannin jam'iyyar PDP a ƙaramar hukumar Kabba/Bunu, jihar Kogi sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki kuma gwamna Yahaya Bello ya karɓe su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel