Uwar Gidan Shugaban Kasa, Remi Tinubu, Ta Shiga Ofis, Ta Fara Aiki

Uwar Gidan Shugaban Kasa, Remi Tinubu, Ta Shiga Ofis, Ta Fara Aiki

  • Matar shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta fara shiga ofishin 'First Lady' jiya Litinin, 5 ga watan Yuni, 2023
  • Misis Tinubu, ta ziyarci manyan ofisoshin sashinta domin ganin yadda komai ke tafiya tare da babban sakataren gidan gwamnati
  • A ranar 29 ga watan Mayu, aka rantsar da mijinta, Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban Najeriya

FCT Abuja - Uwar gidan shugaban ƙasa "First Lady," Sanata Oluremi Tinubu, ta shiga ofishinta domin fara aiki a matsayin mace lamba ɗaya a Najeriya ranar Litinin, 5 ga watan Yuni.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Misis Tinubu ta isa bangaren matar shugaban ƙasa bisa rakiyar masu tsaronta a Villa da ke birnin tarayya Abuja.

Oluremi Tinubu.
Uwar Gidan Shugaban Kasa, Remi Tinubu, Ta Shiga Ofis, Ta Fara Aiki Hoto: Sen. Oluremi Tinubu
Asali: Facebook

Daga zuwanta, ta samu kyakkyawar tarba daga babban Sakataren fadar shugaban ƙasa, Mista Tijjani Umar, da shugabannin ɓangarorin sashin matar shugaban ƙasa.

Wane aiki matar shugaba Tinubu ta fara yi a ranar farko?

Daga nan, matar shugaban ƙasa ta fara tafiya rangadi domin duba ofishin da ke ɓangarenta, wanda ya haɗa da ofishin shugabanci, ICT, shirye-shirye, midiya da kuma ofishin tsara ayyuka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An haifi Oluremi Tinubu a ranar 21 ga watan Satumba, 1960, mahaifiyarta yar kabilar Itsekiri ce yayin da mahaifinta ya kasance bayerabe.

Ta yi aiki a matsayin matar gwamnan jihar Legas tsakanin 1999 zuwa 2007, daga nan kuma ta lashe zaɓen Sanata mai wakiltar Legas ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya.

Sanata Oluremi Tinubu ta shiga harkokin taimako da ba da tallafi da dama da nufin sanya walwala da jin daɗi a fuskokin mutane masu ƙaramin karfi a mazaɓarta.

Ta taɓa haɗa gasar karanto haruffan kalma da aka fi sani da, "Spelling Bee competition," a tsakanin daliban sakandiren jihar Legas wanda ya samar da gwamnan rana ɗaya a zangon mulkin mijinta.

Mai gidanta, Bola Ahmed Tinubu, ya samu nasarar lashe zaben shugaban ƙasa wanda ya gudana a watan Fabrairu kuma aka rantsar da shi ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa da Wike, Umahi da Akpabio a Villa

A wani labarin kuma Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da tsoffin gwamnoni 3 a fadarsa da ke birnin Abuja.

Rahoto ya nuna tsohon gwamnan Ribas, Nyesom Wike, tsohon gwamnan Ebonyi, Dave Umahi da Godswill Akpabio sun isa Villa da karfe 2:33 na ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel