NSA, CBN: Hadimin Atiku Ya Lissafa Jerin Mukamai 5 Da Bai Kamata Tinubu Ya Baiwa Yan Siyasa Ba

NSA, CBN: Hadimin Atiku Ya Lissafa Jerin Mukamai 5 Da Bai Kamata Tinubu Ya Baiwa Yan Siyasa Ba

  • Daniel Bwala, kakakin Atiku Abubakar, ya shawarci Shugaban kasa Bola Tinubu kan kafa majalisarsa, musamman ya lissafo mukamai biyar da bai kamata a ba yan siyasa ba
  • Bwala ya yi gargadi kan nada yan siyasa a mukamai irinsu Mai ba kasa shawara kan tsaro, Ministan tattalin arziki da sauransu
  • Shugaban kasa Bola Tinubu wanda aka rantsar a ranar 29 ga watan Mayu ya riga ya fara nade-nade a majalisarsa

Daniel Bwala, kakakin Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2023, ya shawarci shugaban kasa Bola Tinubu game da kafa majalisarsa.

Bwala ya lissafa wasu mukamai biyar da yake ganin bai kamata a baiwa yan siyasa su ba a gwamnatin Tinubu.

Shugaban kasa Bola Tinubu da mai saronsa a baya
NSA, CBN: Hadimin Atiku Ya Lissafa Jerin Mukamai 5 Da Bai Kamata Tinubu Ya Baiwa Yan Siyasa Ba Hoto: @BwalaDaniel
Asali: Twitter

Jigon na PDP ya ba da shawarar ne a cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter wanda Legit.ng ta gano a ranar Asabar, 3 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Ba haka ake ba: Atiku ya ankarar da Tinubu kan yadda ake cire tallafin fetur, ya caccaki tsarinsa

Ya rubuta:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Babban gwajin lamba na 16 zai kasace nadin wadannan;
1. Mai ba kasa shawara kan harkokin tsaro
2. Ministan tattalin arziki
3. Darakta Janar na SSS da NIA
4. Ministan man fetur
5. Gwamnan babban bankin Najeriya
"Kada ya kuskura ya nada dam siyasa kan wadannan mukamai, idan ba haka ba zai maimaita tarihi."

Shugaban kasa Tinubu wanda aka rantsar a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu a Abuja, ya sanar da nade-nadensa na farko.

Zamfara: Gwamnan PDP Lawal Ya Ba Tsohon Gwamnan APC Wa’adin Kwanaki 5

A wani labari na daban, Dauda Lawal Dare, sabon gwamnan jihar Zamfara, ya ba tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle wa'adin kwanaki biyar ya dawo da motocin gwamnati da jami'ansa suka tafi da su yayin da yake matsayin gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

“Sai An Tauna Tsakuwa Idan Za a Kai Najeriya Gaba”: Wike Ya Goyi Bayan Tinubu Kan Cire Tallafin Mai

A cewar jaridar Daily Trust, Lawal, wanda ya kasance zababben gwamna karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya bayar da wa'adin ne a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Sulaiman Bala Idris ya saki.

Lawal ya bayyana cikakkun bayanai a kan motocin da ake zargin sun yi batan dabo, yana mai cewa zai dawo da kudaden da gwamnatin Matawalle ta sace da kuma kayayyakin gwamnatin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel