Zamfara: Gwamnan PDP Lawal Ya Ba Tsohon Gwamnan APC Wa’adin Kwanaki 5

Zamfara: Gwamnan PDP Lawal Ya Ba Tsohon Gwamnan APC Wa’adin Kwanaki 5

  • Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ba tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle wa'adin kwanaki 5 ya dawo da motocin da ake zargin ya wawure
  • Lawal, wanda aka zaba karkashin inuwar jam'iyyar PDP, ya yi zargin cewa tsohon gwamnan na PDP bai da wani aiki guda na nunawa a shekaru 8 amma ya tatse asusun jihar
  • Gwamnan na PDP ya nuna jajircewar gwamnatinsa na kwato dukkan kudade da kayayyakin da aka sace daga gwamnatocin baya

Gusau, Zamfara - Dauda Lawal, sabon gwamnan jihar Zamfara, ya ba magabacinsa, Bello Matawalle wa'adin kwanaki biyar ya dawo da motocin gwamnati da jami'ansa suka tafi da su yayin da yake matsayin gwamnan jihar.

A cewar jaridar Daily Trust, Lawal, wanda ya kasance zababben gwamna karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya bayar da wa'adin ne a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Sulaiman Bala Idris ya saki.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Bayanai Sun Bayyana Yayin da Atiku, Makinde Da Magajin Wike Suka Sa Labule

Bello Matawalle da Dauda Lawal
Zamfara: Gwamnan PDP Lawal Ya Ba Tsohon Gwamnan APC Wa’adin Kwanaki 5 Hoto: Bello Matawalle, Dauda Lawal
Asali: Twitter

Lawal ya bayyana cikakkun bayanan kudade da kayayyaki da Matawalle, tsohon gwamnan Zamafara ya sace

Lawal ya bayyana cikakkun bayanai a kan motocin da ake zargin sun yi batan dabo, yana mai cewa zai dawo da kudaden da gwamnatin Matawalle ta sace da kuma kayayyakin gwamnatin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin ta bayyana wani jawabi da Matawalle, wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar karkashin jamiyyar All Progressives Congress (APC) ya yi a matsayin makirci da kokarin janye hankalin gwamnatin PDP, rahoton Thisday.

Lawal ya ce ba zai yi cacar baki da gwamnatin APC da ta shafe watanni 4 kan mulki ba tare da aiki guda da mutanen jihar suka amfana ba.

Lawal ya ce yana da hujjoji cewa Matawalle ya sace kudade da kayayyakin jihar Zamfara

Ya kara da cewar akwai hujjoji a hannunsa da zai kwancewa tsohon gwamnan zani a kasuwa kuma ya bayyana barnarsa.

Kara karanta wannan

Jihar Ondo: Sabon Bayani Ya Bayyana Kan Halin Da Lafiyar Gwamna Akeredolu Ke Ciki

A cewar gwamnan na Zamfara, Matawalle ya ba da kwangilar ayyuka na N1,149,800,000.00 ga wani kamfani Hafkhad Properties and Facilities Management Nig. LTD don siyar motoci da za a rabawa manyan masu ruwa da tsaki, ma'aikatu, sassa da hukumomin gwamnati.

Wani bangare na jawabin ya ce:

"Gwamnatinmu ta jajirce wajen cika alkawaran yakin zabe da ta daukarwa mutanen kirki na jihar Zamfara wanda ya kunshi gaggauta kwato kudade da kayayyakin gwamnati da aka sace."

Ban ayyana triliyan N9 a matsayin kadarorina ba, Lawal Dare

A wani labarin, mun kawo a baya cewa Gwamna Dauda Lawal Dare na jihar Zamfara, ya yi watsi da rahotannin cewa ya ayyana naira tiriliyan 9 na tsaba, kadarori da hannun jari da yake da su.

Da yake magana a ranar Alhamis, 1 ga watan Yuni a wata hira da sashin Hausa na Radiyo Faransa (RFI), Lawal ya ce makirai ne suka kirkiri rade-radin da ke yawo

Asali: Legit.ng

Online view pixel