Gwamnatin Ondo Ta Karyata Rade-Radin Mutuwar Gwamna Rotimi Akeredolu

Gwamnatin Ondo Ta Karyata Rade-Radin Mutuwar Gwamna Rotimi Akeredolu

  • Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo yana nan da ransa cikin koshin lafiya kuma yana aiki yadda ya kamata
  • Gwamnatin Ondo ta yi martani a kan rade-radin da ke yawo a soshiyal midiya na zargin mutuwar gwamnan jihar
  • Ta ce gwamnan yana dan fama da rashin lafiya amma yana gudanar da hakokin da suka rataya a wuyansa yadda ya kamata

Ondo - Gwamnatin jihar Ondo ta bayyana jita-jitan mutuwar Gwamna Rotimi Akeredolu a matsayin karya, TVC News ta rahoto.

Har ila yau, gwamnatin ta kuma bukaci jama'a da su yi watsi da wannan jita-jita domin a cewarta kanzon kurege ne.

Gwamna Rotimi Akeredolu
Gwamnatin Ondo Ta Karyata Rade-Radin Mutuwar Gwamna Rotimi Akeredolu Hoto: @kc_journalist
Asali: Twitter

A cikin wata sanarwa da kwamishinan labarai na jihar, Bamidele Ademola-Olateju ya fitar, ya ce wasu wasu na son cin ribar siyasa ta yada labarai da ke kau da mutane daga kan hanya.

Kara karanta wannan

Rigima Sabuwa: Gwamnan PDP Zai Yi Binciken Kwakwaf Kan Gwamnatin Da Ya Gada, Ya Bayyana Dalilansa

Gwamna Akeredolu na kula da harkokin jiha yadda ya kamata

Gwamnatin ta bayyana cewa Gwamnan baya jin dadi amma yana kula da harkokin jihar sannan yana bayar da ayyuka ga jami'an gwamnati a inda bukatar hakan ya taso.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jawabin ya kara da cewar,

"An cika mu da yawan kiraye-kiraye da sakonni game da halin da lafiyar Gwamna, Arakunrin Oluwarotimi Akeredolu, SAN, CON yake ciki. Mun zabi yin watsi da wannan mugun kulli har sai da ta kai wasu mutane na son cin ribar siyasa ta yada labarai da ke kau da mutane daga kan hanya
"Koda dai Gwamnan na dan fama da jiki, yana kula da harkokin jihar sannan yana bayar da ayyuka ga jami'an gwamnati a inda bukatar hakan ya taso.
"Muna kira ga jama'a da su yi watsi da jita-jitan. Aketi na nan da rana."

Kara karanta wannan

Shin Sabon Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, Ya Ayyana Triliyan N9 a Kadarorinsa? Gaskiya Ta Bayyana

Jam'iyyun adawa sun nemi sanin halin da gwamnan ke ciki

Shafukan soshiyal midiya sun cika da labarin mutuwar Gwamna Akeredolu a yan baya-bayan nan.

Hakan ya sa jam'iyyun adawa a jihar neman gwamnati ta bayyana halin da lafiyar gwamnan ke ciki, rahoton Vanguard.

Da yake martani ga rashin bayyanan gwamnan a taro tsawon makonni, shugaban jam'iyyar Social Democratic Party, Stephen Adewale, ya koka kan halin da lafiyarsa ke ciki.

A nasa bangaren, sakataren labaran PDP, Kennedy Peretei, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya bukaci wadanda ke boye gwamnan da su fito su fada ma mutane inda yake don fitar da jihar daga duhu.

Yan daba sun farmaki ayarin motocin gwamna Yahaya Bello

A wani labari na daban, mun ji cewa yan daba sun farmaki ayarin motocin gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, wanda ke a hanyarsa ta dawowa daga Abuja zuwa Lokoja.

Kwamishinan labarai da sadarwa na jihar, Kingsley Femi Fanwo, ya yi zargin cewa wasu mutane da ake tunanin magoya bayan Alh Muritala Yakubu Ajaka ne sun tare ayarin gwamnan sannan suka farmake su.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel