Babu Sa'a: Mutane Sun Fadi Ra'ayinsu Yayin Da Ruwan Sama Ya Cika Inda Tinubu Zai Karbi Rantsuwa

Babu Sa'a: Mutane Sun Fadi Ra'ayinsu Yayin Da Ruwan Sama Ya Cika Inda Tinubu Zai Karbi Rantsuwa

  • Wurin taron bikin rantsar da Bola AhmedTinubu da mataimakinsa Kashim Shettima ya samu tasgaro saboda ruwan sama
  • An samu mamakon ruwan sama da aka yi da sanyin safiyar yau Litinin 29 ga watan Mayu a cikin birnin taraya Abuja
  • A wani faifan bidiyo da ya karade kafar sada zumunta, an gano inda Bola Tinubu zai karbi rantsuwa ya cika da ruwa

FCT, Abuja – An tafka ruwan sama a wurin taron bikin rantsarwa na shugaban kasa a yau Litinin 29 ga watan Mayu.

A wani faifan bidiyon da ya karade kafar sada zumunta wadda Legit.ng ta samo, an gano inda zababben shugaban kasa da mataimakinsa za su karbi rantsuwa a cike da ruwa saboda mamakon ruwan sama da aka samu da sanyin safiya.

Bola Tinubu
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Har ila yau, an gano wasu ma’aikata a wurin taron suna ta kokarin kwashe ruwan don samun damar gabatar da taron ba tareda wata matsala ba.

Kara karanta wannan

Matakalar Taron Rantsar da Abba Gida Gida Ta Rushe Yayin Bikin Rantsar da Shi a Kano

Mutane sun bayyan ra'ayinsu mabambanta game da ruwan saman

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu a kafar sada zumunta ta Twitter, inda suka bayyana mabambantan ra’ayi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

@EkizDavis:

“Ba sa’a, watakila ba zai karbi rantsuwar ba.”

@Akanbi_Semilore:

“Ruwan sama ai albarka ne. Ka yi addu’ar fari a gidanku. Ruwan sama albarka ne ga kasa gaba daya.”

@IloriId:

“A yankin Yarbawa, ruwan sama a lokacin biki hakan na nuna albarka ne, ya na nuna an wanke datti saboda samun sabuwar gwamanti, Allah ya taimaki sabon shugaban kasa da kuma Najeriya.”

@danganausman:

“A irin guntun tunanika, lokacin da ake ruwan sama, shi ne babu sa’a ko? ka ji makiyan Najeriya. Ka ci gaba da korafi har wasu shekaru 4.”

Dalilin Da Yasa Bai Kamata A Rantsar Da Tinubu Ba, Datti Baba-Ahmed Ya Bayani

Kara karanta wannan

A banza: Peter Obi ya fadi abin da zai faru dashi bayan an rantsar da Tinubu

A wani labarin, Mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Datti Baba-Ahmed ya bayyana yadda kundin tsarin mulki ya yi bayani akan rantsar da Bola Tinubu.

Ana saura kwana hudu kenan kafin a rantsar da Tinubu, Datti ya ce zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Faburairu da ya kawo shugaban kasa Tinubu, akwai kura-kurai a ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel