ku Ci Gaba da Zama Kan Mukamanku Har Zuwa Ranar Karshe, Buhari Ga Ministoci

ku Ci Gaba da Zama Kan Mukamanku Har Zuwa Ranar Karshe, Buhari Ga Ministoci

  • Shugaba Buhari ya yi bankwana da Ministoci a taron ƙarshe da ya jagoranta ranar Laraba 24 ga watan Mayu, 2023
  • Muhammadu Buhari ya faɗa wa ministocin su koma Ofis su ci gaba da tafiyar da ayyukansu har zuwa ranar 29 ga watan Mayu
  • Ministan yaɗa labarai, Alhaji Lai Muhammed ya musanta rahoton da aka fara yaɗawa cewa Ministoci sun sauka daga kujerunsu

Abuja - Shugaban ƙasa mai barin gado, Muhammadu Buhari, ya umarci kafatanin Ministocinsa su ci gaba da ayyukan Ofisoshinsu har zuwa ranar ƙarshe da wa'adin gwamnatinsa zai ƙare.

Daily Trust ta tattaro cewa shugaba Buhari zai miƙa ragamar mulkin Najeriya ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Aaiwaju Bola Ahmed Tinubu, ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, 2023.

Taron FEC.
ku Ci Gaba da Zama Kan Mukamanku Har Zuwa Ranar Karshe, Buhari Ga Ministoci Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Sakamakon haka wasu rahotanni suka fara yawo cewa shugaban ya sallami dukkan mambobin majalisar Ministoci su sauka daga muƙamansu a wurin taron bankwana.

Kara karanta wannan

Abun Hawaye: Shugaba Buhari Ya Faɗa Wa Ministoci Kalamai Masu Ratsa Zuciya A Taron Bankwana

Amma yayin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron FEC yau Laraba, Ministan yaɗa labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammad, ya ce rahoton ba gaskiya ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya umarci baki ɗaya ministoci su koma Ofisoshinsu, su ci gaba da ayyukan sauke nauyin talakawa da ya rataya a kansu, rahoton Channels tv ya tabbatar.

A kalamansa, Ministan yaɗa labarai ya ce:

"Labarin da aka fara yaɗa wa cewa an rushe majalisar Ministoci ba gaskiya bane, har yanzu ba'a rushe majalisar zartarwa ba. Shugaban ƙasa ya bamu umarnin kowa ya koma.ofishinsa."
"Saboda haka babu ƙanshin gaskiya a labarin cewa an rusa majaliaar zartarwa ta Ministoci, har yanzu tana nan a kan aiki, duk wani labari da ake yaɗawa karya ne, an bamu umarnin mu koma.Ofis."
"Kuma ina da yakinin cewa zamu ci gaba da aiki har zuwa ranar 29 ga watan Mayu, 2023, sabida haka rokon dan Allah ku yi watsi da labarin ƙanzon kurege."

Kara karanta wannan

Shin Buhari Ya Canja Tunani Zai Zauna a Abuja Ya Taimaka Wa Tinubu? Ya Faɗi Gaskiya da Bakinsa

Ina Fatan Daura Ba Zata Muku Nisa Ba Bayan Mun Sauka Mulki, Buhari Ga Ministoci

A wani labarin kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya faɗi kalaman bankwa maau shiga rai a taron FEC na karshe ranar Laraba.

Shugaba Buhari ya jagoranci taron FEC na bankwana da Ministoci yau Laraba. Ya yi kalamai masu ratsa zuciya game da rayuwa bayan sauka daga kujera lamba ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel